Dan asalin Jihar Kano, Dakta Mubark Mahmud, PhD, wanda yake zaune a kasar Faransa, ya kirkiro wata dabarar auna tsayin bishiyu, wanda a halin yanzu an sanya wa manahjar suna “Mahmud Method.”.
An saka a manhajar M-Tree da jami’o’i a Faransa ke amfani da ita wajen auna tasayin bishiya da kaurinta. An kaddamar da sabuwar fasahar a hukumance a Jami’ar Paris-Saclay a ranar 30 ga Afrilu, kuma an buga ta a cikin mujallar ‘Smart Agricultural Technology,’ tare da tsare-tsaren hadawa cikin manhajojin ilimi a cibiyoyi daban-daban.
- Yawan Wutar Lantarkin Da Sin Ke Iya Samar Ta Amfani Da Karfin Ruwa Ta Kai Matsayin Koli A Duniya
- Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Faransa
Har ila yau, akwai niyyar habaka bincike ta hanyar kirkirarriyar fasaha. Shahararren hamshakin attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya yaba wa Dakta Mahmud a yayin wani taron da aka gudanar a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, inda ya bayyana nasarar da ya samu a matsayin babbar karramawa ga Jihar Kano da Nijeriya.
Ya ce,”Ya kamata Kano ta yi alfahari da na’urar auna tsayin bishiya da Dakta Mubarak ya yi, wanda gwamnatin Faransa ta amince da ita a hukumance.
“Na’urar Dakta Mahmud tana amfani da fasahar zamani don auna bishiyu, tana samar da ingantacciyar hanyar kula da muhalli da kula da gandun daji, wanda ke nuna darajar tallafa wa masu basirar gida a ci gaban kimiyya.”
An dai haifi Dakta Mubarak a Unguwar Hausawa Masallacin Murtala, da ke Karamar Jukumar Kumbotso ta Jihar Kano a Nijeriya.
Ya yi karatun Firamare a Hausawa Model ta Jihar Kano; ya yi karatu a Kwalejin Kimiyya ta jeka ka dawo a Kano; daga nan ya tafi zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudi, inda a nan ne ya samu digiri na farko.
Ya samu digiri na biyu a fannin noma da gandun daji; sannan ya samu digirin-digirgir kan Agro Paris Tech, Paris, a Kasar Faransa, ya sake yin karatun digiri na biyu a fannin sanin yanayi, Amfanin Kasa da Ayyuka na Muhalli; ya kuma samu digirin-digirgir a Jami’ar Paris a fannin Ecology.
Ya yi aiki a Cibiyar Bincike ta Kasa ta Faransa ta Noma, Abinci da Muhalli a matsayin jami’i (Mai bincike); Lakca a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp