Wani dan bindiga ya harbe mutane uku har lahira tare da raunata akalla wasu shida a wata mashaya da ke jihar California ta Amurka a ranar Laraba, in ji ‘yan sanda.
Shima dan bindigar ya mutu a lamarin, inda ‘yansandan suka bayyana cewa, an yi batakashi ne da wasu jami’an ‘yansanda da ke wurin amma babu wani jami’in da ya samu rauni.
“An tabbatar da mutuwar mutane 4 a wurin ciki har da dan bindigar, An kai mutum 6 zuwa asibiti, 5 sun samu raunukan harbin bindiga.” in ji ‘yansandan Sheriff
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp