Dan kasar China, Geng Quangrong da ake zargi da kashe masoyiyarsa ‘yar Nijeriya, Ummukulsum Sani Buhari, ya musanta tuhumar da ake masa a gaban wata babbar kotun Kano da ke kan titin Miller, karkashin mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji.
A zaman da ya gabata, kotun ta dage sauraron karar saboda rashin samun mai fassara, wanda ake tuhumar ya yi ikirarin cewa ba ya jin Turanci.
A ci gaba da zaman, lauyan gwamnati karkashin jagorancin babban lauya mai shigar da kara na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawal, ya samo wa kotun wani mai fassara daga ofishin jakadancin kasar China dake Nijeriya, Mista Guo Cumru.
Ayau, lauya mai shigar da kara ya shigar da karar da ake tuhumar wanda ake tuhumar a karkashin sashe na 123 sub 1a na dokar shari’a ta jihar Kano kamar haka:
“Kai Geng Quangrong mai zama a rail way Quarters a Kano, a ranar 16 ga Satumba, 2022 da misalin karfe 21:00, ka je wani gida a Janbulo Quarters da ke karamar hukumar Gwale a Kano, ka yi kisan gilla wanda hukuncin kisa ne ya cancanci wanda ya aikata hakan.
“Ka yi sanadin mutuwar Ummukulsum Sani Buhari ta hanyar daba wa Ummukulsum wuka a sassa daban-daban na jikinta tare da sanin cewa yin hakan, zai yi sanadin mutuwarta. Sabida haka, ka aikata laifi 221(b) na dokar penal code wacce aka yi wa kwaskwarima.”
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta tuhumar da ake masa.
Babban Lauyan ya roki kotun da ta dage sauraron karar zuwa nan da mako biyu masu zuwa domin ba su damar bayar da shaida a ranakun 14, 15 da 16 ga watan Nuwamba.