Dan wasan gaban Super Eagles na Nijeriya Victor Boniface na ci gaba da haskakawa a kungiyarsa ta Bayer Leverkusen da ke buga gasar Bundesliga ta kasar Jamus.
Dan wasan mai shekaru 22 zai fafata da dan wasan tsakiya na RB Leipzig Xavi Simons da kuma dan wasan gaba na Hoffenheim Maximilian akan kyautar gwarzon dan wasan Bundesliga na watan Satumba.
- Kotu Ta Kori Sylva Dan Takarar Gwamnan APC A Bayelsa
- An Kama Masu Laifi 537, An Daure 250 Cikin Wata 3 A Borno
Boniface ya zura kwallaye biyu kuma ya taimaka an zura kwallaye uku a wasanni hudu da ya buga wa Bayer Leverkusen a watan Satumba.
Boniface yana jin daɗin rayuwa a babbar gasar Jamus bayan zuwansa daga kungiyar kwallon ƙafa ta Belgian Pro League Union St. Gilloise.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp