Majalisar dokokin Jihar Kogi ta koka da rashin tsaro da ke kara ta’azzara a cikin makonni uku da suka gabata a Karamar Hukumar Yagba ta Gabas ta jihar.Â
Memba mai wakiltar mazabar Yagba ta Gabas a majalisar dokokin Jihar Kogi, Hon. Emmanuel Obaro, ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya gabatar da kudirin gaggawa kan lamarin a majalisar.
- Babu Farfesan Bogi A Jami’ar Bayero Ta Kano – Shugaban Jami’a
- Bayan Ganawa Da Mohammed Bello Koko, Ma’aikatan NPA Sun Janye Shiga Yajin Aiki
Hon. Obaro, wanda ba zai iya tabbatar da kubutar wadanda aka sace ba, ya ce batun yin garkuwa da mutane da fashi da makami na kara kamari a mazabarsa.
Dan majalisar ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta binciki yadda ake samun karuwar yin fashi da makami da garkuwa da mutane tare da kawo karshen lamarin.
Sai dai ya yabawa gwamnan Jihar, Yahaya Bello bisa yadda yake kokarin tabbatar da tsaro a jihar.
Dan majalisar ya bukaci kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da ya yi mu’amala da sabbin shugabannin kananan hukumomin da aka nada don tsara hanyar da za ta magance matsalar rashin tsaro a fadin jihar.