A ranar Lahadin da ta gabata ce, dan majalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Funtuwa Hon, Alhaji Abubakar Mohammed Total ya gwan-gwaje al’ummar mazabunsa da kayan abincin azumi na kimanin zunzurutun kudi har naira miliyan 45,400,000.
Taron rabon tallafin ya samu halartar manyan ‘yan siyasar na jam’iyyar APC, maza da mata da sauran al’ummar karamar hukumar Funtuwa da kewayenta. Taron ya gudana ne a harabar kofar gidan dan majalisar da ke unguwar Magajin Makera a cikin garin Funtuwa.
- Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
- 2027: An Buga Gangar Neman Tazarcen Tinubu A Arewa
Wadanda suka amfana da tallafin sun hada da ‘yan siyasar na jam’iyyar APC maza da mata na mazabunsa da ke shiyar Funtuwa da marayu da marasa karfi da sauran mabukata.
Wadanda suka amfana da tallafin sun tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan tallafi da Allah Ubangiji ya ba su, inda suka nuna godiya godiya da kuma fatan alheri da jinjina wa dan majalisar kan wannan tallafi na kayan abincin azumi.
Sannan kuma sun shawarci dan majalisar da cewa, idan Allah ya kai kakar siyasa mai zuwa, ya nemi kujerar majalisar wakilai domin ya cancanta.
Daya daga cikin dattawan APC a yankin Funtuwa, Alhaji Usman Alaliya Funtuwa ya yi tsokaci dangane da al’amarin, inda bayyana cewa farin cikinsa dangane da wannan tallafi. Ya yi wa dan majalisar fatan alheri tare da jawo hankalinsa kan ya kara kokari a wajen wanzar da irin wadannan ayyukan na alheri ga al’ummar mazabunsa na shiyar Funtuwa.
A jawabinsa na godiya a wurin taron, dan majalisar dokokin ya bayyana godiya ga al’ummar Funtuwa, ya ce zai ci gaba da kawo ayyukan alheri tare da abubuwan jin dadin more rayuwar ga al’ummar mazabunsa na Funtuwa da kewayenta gaba daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp