Dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Bauchi a mazabar Toro/Jama’a a jam’iyyar NNPP, Ibrahim Garba Tilde, ya nemo tallafin Naira miliyan 20 ga Kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa Iqamatussunnah (JIBWIS), da ke Tilden Fulani a Karamar Hukumar Toro don sayen filin gina masallacin Idi da makaranta.
Da ya ke mika kudin ga kungiyar, ya shaida cewar hakan na cikin kokarinsa na nemo ci gaba ga al’ummar mazabar.
- Xinjiang Ta Soki Matsayar Amurka Ta Sanya Wani Kamfanin Fasaha Cikin Jerin Kamfanonin Da Ta Kakabawa Takunkumi
- Ba Tsige Ni Aka Yi Ba, Ni Na Yi Murabus Da Kaina – Baba Impossible
Ya ce, tallafin an nemo ne domin kungiyar ta samu mallakar filin Idi na dindindin tare da samun damar karasa makarantar da ake ginawa a Tilde.
A cewarsa, ba ya son a bayyana sunansa amma ya yi hakan ne domin Allah don ya taimaka tare da yin fatan za su yi amfani da kudaden ta hanyoyi da suka dace.
Tilde ya bai wa kungiyar da al’ummar mazabarsa tabbacin cewa baya ga gyaran fanfunan tuka-tuka guda 100 da ya yi, zai ci gaba da jawo hankalin masu tallafi domin su kawo tallafinsu wannan yankin.
Ya ce, wannan somin tabi ne domin idan ya samu damar zama dan majalisa zai tabbatar ya kyautata rayuwar al’ummar mazabarsa.
Da ya ke amsar kudaden a madadin kungiyar, shugaban JIBWIS reshen Tilde, Malam Abdullahi Muhammad, ya nuna matukar godiyarsu bisa hakan tare da tabbatar da cewa za a yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace.
Ya ce, kungiyar a wannan matakin ba ta taba amsar maguden kudade a matsayin tallafi, don haka ya mika godiyarsu kan hakan tare da addu’ar Allah saka wa wanda ya yi wannan tallafin.
Ya misalta Ibrahim Tilde a matsayin mai hidima ga Addini.