Dan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar P.R.P., Salisu Tanko Yakasai (Dawisun Kanawa, Ya kaddamar da Kudure-kuduren takararsa ta gwamna a zaben 2023.
Salisu Tanko, ya ce Kudure-Kuduren ya dauke su tsawon shekaru suna tattara bayanai na aiyuka da manufofin da suke ganin idan aka aiwatar da su jihar Kano zata bunkasa fiye da yadda take a yanzu.
- 2023: Shin Ko Abba Gida Gida Bana Bai Shirya Wa Mulkin Jihar Kano Ba Ne?
- Masoyan Takai Da Gawuna Za Su Mara Wa Tinubu A 2023
Yakasai ya bayyana cewa, sun fara wannan aiki tun shekaru kusan bakwai, a sannan ma basu san Allah zai tsaida shi a matsayin dan takarar Gwamnan jihar Kano ba.
Kudure-Kuduren sun kunshi bayanai akan fanni guda bakwai wanda suke ganin suna da alaka ta kud-da-kud da doron manufofin jam’iyarsu ta PRP, wanda suka hada da:
1- Karfafa karfin tattalin arzikin jihar Kano
2- Inganta harkar ilimi
3- Inganta harkar lafiya
4- Inganta harkar muhalli
5- Inganta manyan aiyuka
6- Inganta aikin gwamnati
7- Inganta harkar tsaro da zaman lafiya
A Jawabin nasa ya bayyana cewa, hakika duk wanda yake neman shugabanci ya kamata a same shi cikin shiri na tsare tsaren da idan Allah Ya ba shi dama zai aiwatar.
Yaksai ya ce hakan yasa su ne na farko a jihar Kano a cikin yan takarar gwamna da suka fitar da Kudure-Kudure domin al’umar jihar Kano su duba suga abinda muka tanadar musu.
Zaku iya sauke wannan Kudure-Kuduren daga shafinsu na www.dawisu.com domin dubawa.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyar PRP na jihohin Kano da Kaduna da Jigawa, da yan takarar Gwamnan PRP na Jihohin Kaduna, Adamawa, Gombe da Jigawa. Haka kuma shugabannin kungiyoyi daban daban sun samu halarta, tare da sauran al’umar jihar Kano.