Dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar NNPP, Engr Nura Khalil ya tallafa wa ‘yan gudun hijirar jihar da kudi Naira Miliyan 50 domin rage musu wahalhalun da suke sha.
Dama dai Engr. Nura Khalil ya kafa wata gidauniya mai suna Nurakhalil Foundation wadda mai dakinsa Hajiya Farida Barau take jagoranta. Gidauniyar ta fi karfin shekara goma (10) da kafuwa inda har kullum take aikin taimakon marayu da ‘yan gudun Hijra, da taimakawa ga matasa maza da mata wajen karatunsu.
Ganin yadda ‘yan gudun hijrar ke shan wahalhalu, babu wajen kwana mai kyau sannan ga barazanar yunwa ta har sai sun fita sun yi barar abin da za su ci da iyalansu, wasu ma sun fadi cewa sai an yi fasikanci da su ake ba su abin da za su kai ma iyalansu, ya sa Engr Nura Khalil ya ware Naira Miliyan Hamsin (50,000,000) domin ganin ‘yan hijirar sun wadatu da abinci da tufafi.
A zantawarsa da aka yi da shi, Khlalil ya bayyana cewa idan har mutum zai iya mika kudinsa ya sayi form din takara to shi a nashi tunanin gara ya taimaka ma wadannan bayin Allah da iftila’i ya fadama wa, “kana ji kana gani a raba ka da gidanka, wasu an kashe su, wasu kuma an sace su har yau babu labarinsu.” Ya bayyana.
Ya jajanta ma al’ummar Jihar Katsina baki dayan su a kan fargaba da har kullum suke kwana suke tashi da shi a zukatansu. Kana ya ba da shawarar kowa ya dukufa ga yin addu’a ba dare babu rana har Allah ya kawo ma Jihar Katsina sauki.
Tuni dai kwamitin da aka kafa domin raba tallafin ya dukufa gudanar da aikin tsara rabon inda ake sa ran ‘yan gudun hijira na sassa daban-daban na Jihar Katsina su amfana.