Shahararren mawakin nan kuma dan rawa na kasar Amurka, Tito Jackson, wanda ya kasance daya daga cikin ‘yan biyar kuma dan uwa ga mawaki Michael Jackson da ‘yar uwarsa Janet, ya mutu yana da shekara 70 a duniya, kamar yadda dansa ya tabbatar.
A cikin sanarwar da dan na say a fitar a shafinsa na D, ya bayyana cewa mahaifin nasu ya mutu, bayan yasha fama da jiyya, kamar yadda ya bayyana, sannan ya bayyana cewa mahaifin na su mutumin kirki ne kuma za su yi kewarsa.
- Mun Samu ‘Yan Takara Masu Tu’ammali Da Miyagun Kwayoyi – Hukumar Zaben KadunaÂ
- Jerin Kasurguman ‘Yan Bindiga Da Sojoji Suka Hallaka A ArewaÂ
Kamar yadda dan uwan Tito ya tabbatar, ya rasu sakamakon bugawar zuciya a lokacin da yake tuki a ranar Lahadin data gabata a lokacin da yake tafiya daga jihar New Medico zuwa garinsu, jihar Oklahoma, duka a kasar Amurka.
A kwanakin baya ne Tito ya halarci wani bikin rawa a kasar Jamus da Ingila da jihar California ta Amurka tare da ‘yan uwansa guda biyu,
Marlon da kuma Jackie Jackson.
Marigayi Tito yana daya daga cikin ‘yan uwan Michael Jackson su biyar da suka hada da Jackie da Jermaine da Marlon and Michael, wadanda duka sun bayar da gudunmawa sosai wajen nasarar Michael Jackson.
Dan uwansa, Michael Jackson, yam utu a shekara ta 2009 yana da shekara 50 kuma shi ne kusan wanda mutane suka fi sani saboda yadda ya iya rawa da kuma daukakar da ya samu.
A shekarar 1997 ne aka karrama ‘yan uwan su biyar, a Rock and Roll a Amurka, sakamakon nasarar da suka samu tare da tsohuwar jaruma Diana Ross,wadda ta rasu da dadewa.
A shekara ta 2016 Tito ya zama dan uwan Jackson na farko da ya samu lambar yabo tun bayan mutuwar dan uwansu kuma tun daga wancan lokacin zuwa yanzu babu wani abu da daya daga cikinsu ya sake ci a matsayin lambar yabo kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Marigayi Tito yam utu yabar ‘ya’ya guda uku, sannan tsohuwar matarsa itama tana nan, sannan mahaifiyarsu, Dolores, ta mutu tun a shekarar 1994 a jihar Califirnia ta kasar Amurka.