Kotun sharia’r musulunci dake zamanta a filin hoki dake Kano ta umarci mai barkwancin nan na manhajar TikTok, Abubakar Ibrahim da aka fi sani da G-Fresh da ya koma yayi bikon matarsa, sayyada Sadiya Haruna, wadda aka ruwaito cewa tayi yaji.
Kamar yadda kotun ta bayyana, tunda G Fresh bai saki matarsa ba akwai bukatar yayi bikon ta domin ci gaba da zaman aure kamar yadda addinin musulunci ya tsara ga duk wadda tayi yaji.
- Kotu Ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Filato
- Yadda Alakar Sin Da Afirka Ke Kara Bunkasa Kasashen Nahiyar Afirka
Lauya mai kare G Fresh Barr. Fatima Aliyu ta bayyana cewar har yanzu G Fresh na matukar kaunar matar sa wanda hakan yasa ba zai iya rabuwa da ita ba kuma shima G-Fresh din yasha nanatawa a shafinsa na TikTok cewa yana son matarsa kuma ba zai iya rabuwa da ita ba.
Kotun dai ta bayar da daga yau zuwa ranar 10 ga watan Oktoba mai kamawa domin G Fresh ya sulhunta da matarsa Sayyada Sadiya Haruna kuma ta koma su ci gaba da zaman auren su.
A kwanakin baya ne dai aka dinga yada wata jita-jita cewar auren taurarin Tiktok din, Sayyada Sadiya Haruna da G-Fresh Al-Ameen Kano state material ya mutu, sai dai daga baya ya fito ya bayyana cewa auren yana nan daram ba kamar yadda ake ta yayatawa ba.
A ranar 16 ga Yunin da ya wuce ne aka daura auren shahararrun masoyan na TikTok, auren da ya dauki hankulan mutane da dama musamman masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani da suka hada da Facebook da D da kuma TikTok din.
Sai dai Jim kadan bayan tarewar Ango a gidan Amarya kuma sai ta tafi aikin Hajji a kasa mai tsarki wanda hakan tasa G-Fresh kullum ya dinga yada bidiyon sa, yana sambatun shaukin rabuwa da amaryarsa.
Amma bayan dawowar amarya sai ga labari ya cika TikTok da sauran kafafen sada zumunta cewa wai auren taurarin biyu ya mutu inda har ma wasu ‘yan TikTok na cewa wai G-fresh ya yi yaji ne daga gidan Sayyada Sadiya ya koma kwanan shago bayan da aka samu sabani a tsakaninsu.
Amma daga baya kuma aka gano cewa har yanzu Al-ameen G-fresh Kano state material ya na nan a dakin matarsa Sayyada Sadiya Haruna kuma shima ya nanata hakan.
Wasu rahotanni sun ruwaito cewar tun farko Sayyada Sadiya ta mayar da shafinta na TikTok wurin tallata magunagunan gargajiya da take sayarwa kuma ta goge duk wani bidiyo da ta yi a baya ciki kuwa har da bidiyoyin soyayyarsu da Kano state material din.
Sai dai goge bidiyon ne yasa wasu suka fara yada jita-jitar cewa an samu matsala tsakanin ma’auratan guda biyu wadanda soyayyar su ya karade ko ina a shafukan sada zumunta.