Al’umma sun fito sosai domin samun damar kada kuri’a a zaben gwamna da ke gudana a yau Asabar a Jihar Bauchi.
Wakilinmu da ya zagaya rumfuna daban-daban a fadin jihar inda ya ga yadda mutane suka fito sosai domin neman yadda za su samu damar kada kuri’arsu.
- Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutum 2 A Tawagar Gwamnan Katsina A Hanyarsu Ta Zuwa Zabe
- An Samu Jinkirin Rarraba Kayan Zabe A Bauchi
Kazalika, dattibai Maza da mata ba a bar su a baya ba inda suka fito domin neman jefa kuri’a.
Kodayeke an samu jinkirin fara zaben da wuri a wasu rumfuna da dama a fadin jihar Bauchi, amma zaben na tafiya cikin kwanciyar hankali zuwa yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp