Akwai alamun tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP ta Rabi’u Kwankwaso zuwa Jam’iyyar PDP, bayan samun wani sabani da gaza cika wasu alkawura daga bangaren Jagoran Jam’iyyar na kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso.
Mai magana da yawun Sanata Shekarau, Malam Sule Ya’u Sule ya tabbatarwa da kafar yada labarai ta BBC Hausa cewa shakka babu an gaza cika alkawarin da kulla tunda farko tsakanin maigidan nasa da Kwankwaso gabanin shigarsu Jam’iyyar NNPP.
A gefe guda kuwa an jiyo Jagoran Ja’iyyar Sanata Kwankwaso na ikirarin cewa shi dai babu wani sabanin siyasa tsakaninsa da Sanata Shekarau a Jam’iyyar ta NNPP.
Da yake karin haske kan batun da ke yawo a kafafen yada labarai na hana Shekarau wasu kujerun takara ya ba mutanensa sai Kwankwason ya kayar da baki ya ce Shekarau din ya bayar da sunayen mutanen nasa a kure saboda lokacin da hukumar zabe ta bayar na sauya ‘yan takara ya kure.
Malam Shekarau, shi ne ke wakiltar mazabar Sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP a hukumance a wata wasika da shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanta a zaman majalisar a ranar 29 ga watan Yuni.
Wasu rahotanni na bayyana cewa, Sanata Shekarau din na ganawa da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da abokin takararsa Ifeanyi Okowa da da Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyochia Ayu, don ganin tsohon gwamnan ya koma Jam’iyyar PDP.
A ranar Lahadin da ta gabata ma, Shekarau ya kira wani taron gaggawa na majalisar shura kan harkokin siyasarsa tare da sanar da Æ´an majalisar halin da ake ciki.
Idan hai ya yi zamu ci gaba da bibiyar wainar da ake toyawa tsakanin tsagin manyan jagororin siyasar Kanon don jin yadda zata kaya.