• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dangantakar Sin Da Afrika Ta Kai Wani Mataki Da Babu Wanda Zai Iya Lalatawa

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Yayin da ake gab da adabo da shekarar 2022, jajirtattun injiniyoyin Sin da Afrika, sun himmantu ba dare ba rana, domin ganin kammaluwar ginin hedkwatar cibiyar kandagarki da yaki da yaduwar cututtuka ta Afrika wato Afrika CDC.

Duniya ta shaida yadda annoba a wuri kan iya yaduwa cikin kankanin lokaci har ma ta zama barazana ga duniya baki daya. Yadda irin wadannan annoba ke barkewa a Afrika, na bukatar shiri da dauki na gaggawa.

  • Babban Jami’in Africa CDC Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Hadin Gwiwarta A Fannin Sarrafa Rigakafin COVID-19 A Afirka

Yadda Sin ta dauki nauyin ginin hedkwatar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika, gagarumar gudunmawa ce da za ta taimaka wajen kyautata lafiyar al’ummar nahiyar, inda za su shafe lokaci mai tsawo suna cin moriyarsa. Haka kuma, ya sake nuna cewa a ko da yaushe, Sin tana tare da al’ummar Afrika, kuma a shirye take ta share musu hawaye.

Bayan taron ministocin kungiyar FOCAC a shekarar 2018 ne kasar Sin ta bayyana aniyarta ta daukar nauyin ginin hedkwatar cibiyar Africa CDC, tare da sanya dukkan kayayyakin da ake bukata a ciki.

A watan Yulin 2020 ne kuma aka rattaba hannu kan yarjejeniyar ginin. Zuwan aski gaban goshi, ya shaida mana cewa kasar Sin na gudanar da wannan aiki ne yayin da take fama da aikin yaki da cutar COVID-19 a gida da kuma yanayi na rashin tabbas da ake fama da shi a duniya. Wato duk da wadannan kalubale, ba ta yi kasa a gwiwa ko dakatar da aikin ba, sai ma dukufa da ta yi don ganin an kammala shi kamar yadda aka tsara.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

Hakika kasar Sin ta amsa sunanta na babbar kasa kuma babbar yaya, wadda ke burin ganin ci gaban ’yan uwanta kasashe masu tasowa, inda a ko da yaushe, take nacewa wajen aiwatar da ayyuka na gani na fada, masu amfani da al’ummar Afrika ke matukar bukata. Wannan ya kai dangantakar sassan biyu wani matsayi da ba za a iya lalatawa ba.

Mun riga mun san cewa, annoba ba ta san iyakar kasa ko jinsi ba, don haka, tana iya bulla a ko ina. Sai dai, yadda aka shiryawa tunkararta zai ba da damar cin galaba a kanta. Taimakon kasar Sin na ginin hedkwatar da samar da kayayyaki a cikinsa, zai karawa nahiyar Afrika karfin tunkara da yaki da duk wata annoba da ka iya bullowa nan gaba, lamarin da zai rage asarar rayuka da ma dogaro da kasashen waje ta fuskar samar da magunguna ko riga kafi ba, domin mun ga yadda kasashe dake kiran kansu manya, suka yi ta boye alluran riga kafin COVID-19 domin amfanin kansu ba tare da tunawa da wadanda ba su da karfi ba. Haka zalika, wannan cibiya na iya zama wani dandali da kwararrun Sinawa za su taimaka wajen bunkasa kwarewar takwarorinsu na Afrika. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa
Daga Birnin Sin

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025
Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha
Daga Birnin Sin

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Next Post
Sojoji Sun Kai Hari Sansanonin IPOB Sun Kwato Bama-Bamai Da Bindigu A Ebonyi Da Enugu

Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda 8 A Borno

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

November 4, 2025
Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

November 4, 2025
China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.