Kamfanin Simintin Dangote ne ke ɗaukar nauyin baje kolin gidaje na Afrika (AIHS) da za a buɗe ranar Litinin a Transcorp Hilton, Abuja.
Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce baya ga daukar nauyin shirin, kamfanin simintin na dangote yana halartar taron wanda shi ne karo na 19 a jerin tarukan.
Sanarwar da mai magana da yawun kamfanin Anthony Chiejina ya sanya wa hannu, ta ce taron da ake sa ran zai karɓi baƙuncin mahalarta daga ƙasashe 21, ya samar da wani dandali da ba kasafai kamfanin ke mu’amala da su ba da suka shafi manyan ƴan kasuwa a harkar samar da gidaje a faɗin nahiyar.
- Shugaban Nijeriya Na 16: Jan Aikin Da Ke Gaban Jagaban
- Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka
Mista Chiejina ya ce: “Yayin da Baje kolin Gidajen ya tattaro mahalarta sama da 40,000, wadanda suka hada da manyan masana’antu, wakilan gwamnati da masu zuba jari, kamfanin Simintin dangote zai yi amfani da wannan dama wajen baje kolin sabbin kayayyakinsa ga abokan ciniki da masu yanke shawara.”
Sanarwar ta ce, kamfanin ya ci gaba da daukar nauyin shirin baje kolin a tsawon shekaru, yana mai tabbatar da cewa zai ci gaba da hada gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen tallafawa samar da matsuguni a Afirka.
A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki.
Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP).
Ya ce: “Kwarewa da haɗin gwiwa su ne manyan abubuwan da muka a gaba, idan aka yi la’akari da saurin ci gaban fasaha a cikin gine-ginen gidaje, samar da kudaɗe da kuma inganta tsarin.”
Ya ce taken taron na wannan shekara, Maimaita Gidaje Ta Hanyar Sabuntawa, wanda daidai yake da ainihin darajar kamfanin.
Barista Adebayo ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa haɗin gwiwa da kamfanin Simintin dangote zai taimaka wajen magance matsalar ƙarancin gidaje a ƙasar.
Ya ce sama da kashi 82 cikin 100 na mahalartan suna riƙe da matsayi na yanke shawara, tare da tabbatar da masu hulda kai tsaye tare da mutanen da ke da ikon saye.
Idan dai za a iya tunawa, Cibiyar Gine-gine ta Nijeriya (NIOB) da masu ruwa da tsaki a harkar gidaje sun bayyana kamfanin dangote a matsayin daya daga cikin manyan hanyoyin bunƙasa gidaje a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp