Mujallar Forbes da ke bibiyar harkokin masu arzikin duniya, ta ce a yanzu hamshakin biloniyan nan dan kasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ne mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka.
Hakan na nufin Johann Rupert mai shekaru 73, ya doke attajirin dan kasuwa na Nijeriya, Aliko Dangote a yawan arziki wanda a baya yake rike da matsayin.
- Kwastam Ta Tara Biliyan 52.7 A Kano Da Jigawa A 2023
- Ya Kashe Limami Saboda Ya Hana Su Shan Wiwi A Kusa Da Masallaci A Kano
A alkaluman da Forbes ta fitar na baya-bayan nan, a kan arzikin attajirai a kowace rana, darajar arzikin Johann Rupert ta kai dala biliyan 10, yayin da Aliko Dangote aka kiyasta nasa arzikin a kan dala biliyan 9.7.
Dangote, mai shekaru 66, ya koma mataki na biyu a jerin masu arzikin Afirka bayan da dukiyarsa ta yi kasa daga dala biliyan 13.5 zuwa dala biliyan 9.5 a farkon shekarar 2024.
Mujallar ta nuna cewa an samu raguwar kudin hamshaƙan ƴan kasuwa kamar Rabiu Abdussamad da darajar arzikinsa ya kai dala biliyan 5.7 da Mike Adenuga wanda nasa arzikin ya kai dala biliyan 3.1.
Bayanai na cewa raguwar darajar arzikin nasu, ba zai rasa nasaba da yadda darajar naira ke ci gaba da faduwa ba, da kuma wasu matsaloli da suka shafi tattalin arziki.