Attajiri mafi kuɗi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin Habasha domin gina masana’antar takin zamani mai darajar dala biliyan $2.5 a yankin Somali na gabashin ƙasar.
An ƙulla yarjejeniyar ne a Addis Ababa ranar Alhamis, inda Dangote zai mallaki kaso 60% na aikin, yayin da Ethiopian Investment Holdings (EIH) za ta riƙe sauran kaso 40%. Bisa bayanan da aka fitar, aikin zai ɗauki watanni 40 kafin ya kammala, tare da samar da ton miliyan uku na taki a duk shekara. Ana haɗa masana’antar kai tsaye da iskar gas na Calub da Hilala da ke kudu maso gabashin Habasha, domin samar da kayayyaki.
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita
- Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21
A cewar EIH, wannan aikin zai rage dogaro da shigo da taki daga waje, tare da rage matsin tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta wajen samun kuɗaɗen musaya na ƙasashen waje. Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban ci gaba wajen tabbatar da tsaron abinci a Habasha, yana mai cewa za ta samar da ayyukan yi da kuma wadataccen taki ga manoma.
Dangote, wanda ke da masana’antar siminti a ƙasashe 10 na Afrika tare da cibiyar takin zamani mai samar da ton miliyan uku a Nijeriya, ya ce haɗin gwuiwar da aka cimma da Habasha na daga cikin muhimman matakai na tabbatar da burin Afrika na bunƙasa masana’antu da cimma isasshen abinci a nahiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp