Shugaban kamfanin Dangote Aliko Dangote, ya bayyana shirin gina tashar jirgin ruwa na biliyoyin Daloli a Jihar Ogun, wanda zai kasance mafi girma a Nijeriya.
Ya kuma ce ana gina sabbin layuka biyu masu karfin metric ton miliyan 6.0 a duk shekara na kamfanin siminti a Itori, Jihar Ogun.
- Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super Eagles
- El-Rufa’i Ya Yi Kadan Ya Sa Mu Bar Jam’iyyar PDP – Sule Lamido
Dangote ya yi wannan bayani ga majalisar zartarwa ta Jihar Ogun karkashin jagorancin gwamna Prince Dapo Abiodun a wata ziyarar ban girma da suka kai a Abeokuta.
Dangote ya ce “ Ya yanke shawarar zuwa ya sanya hannun jari a Jihar Ogun saboda hangen nesan gwamnatin Yarima Dapo Abiodun da kuma tsare-tsare kyawawa wadanda suka mayar da hankali wajen jawo masu zuba jari, da kuma yanayin da masu zuba jari ke ciki a jihar.”
Ya ce Jihar Ogun na daya daga cikin wuraren da ake zuba jari a Nijeriya, inda ta sanya kanta a matsayin masana’antar ‘mai cin gashin kanta a Nijeriya.
A cewarsa, tun da farko mun kau da kai ga barin sanya hannun jari a shiyyar kasuwanci ta Olokola (OKFTZ), amma saboda manufofinku da kuma yanayin da masu zuba jari ke da shi, ina so in ce mun dawo kuma za mu yi aiki tare da gwamnatin jihar don komawa Olokola, kuma ana shirin gina tashar jiragen ruwa mafi girma a kasar.
Da yake karin haske kan ayyukan da kamfanin ke gudanarwa a Jihar, Dangote ya ce sabbin layukan biyu masu karfin metric tan miliyan 6.0 a kowace shekara na kamfanin siminti an gina su a Itori, yayin da kamfanin siminti na metric ton miliyan 12 a kowace shekara kuma yana nan a Ibeshe.
Bayan kammala aikin, Dangote ya ba da tabbacin cewa, jimillar kamfanonin siminti a jihar za su yi makotaka da metric ton miliyan 18 a duk shekara, wanda zai zama jiha ko yanki mafi girma da ke samar da siminti a Afirka.
“Tare da gudunmawar sauran masu samar da siminti a Jihar, Ogun ta kasance a gaban sauran kasashen Afirka a fannin samar da siminti,” in ji shi.
Dangote ya bayyana cewa kamfanin simintin Dangote ne kan gaba wajen samar da siminti a nahiyar Afirka mai karfin metric ton miliyan 52.0 a duk shekara a fadin nahiyar Afirka.
Ya kara da cewa kashi 70 cikin 100 na simintin ana samar da su ne a Nijeriya, inda kamfanin Obajana da ke Jihar Kogi ke samar da metric ton miliyan 16.25 a duk shekara, wanda shi ne mafi girma a Afirka.
Ya ce zuba jarin da ake yi wajen sarrafa kayayyakin ya sa al’ummar kasar nan ta dogara da kanta wajen samar da siminti, kamar yadda kasar nan ta dogara da kanta wajen samar da taki, inda ake samun rarar kayayyakin da ake samu a kasuwannin ketare, wanda hakan ya sa al’ummar kasar ke samun kudaden musanya da ake bukata.
Yayin da yake lura da cewa burin kamfanin shi ne Nijeriya ta dogara da kanta a duk abin da ake samarwa, Dangote ya bayyana cewa a halin yanzu kamfanin yana biyan bukatun cikin gida na ‘Premium Motor Spirit’ (PMS) daga matatar mai 650,000 a kowace rana a Ibeju-Lekki, da kuma tace man jiragen sama da ‘Likuefied Petroleum Gas’ (LPG).
Ya ce, Nijeriya na kokarin farfado da tattalin arziki; Don haka akwai bukatar kamfanoni masu zaman kansu su kara kaimi ga kokarin gwamnati, yana mai ba da tabbacin cewa kamfaninsa zai ci gaba da nuna imaninsa ga al’ummar kasar da jama’arta ta hanyar zuba jari da nufin kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar.
Da yake mayar da martani, Gwamna Abiodun ya jaddada cewa da kafa kamfanin siminti na Itori, zai samar da metric ton miliyan shida na siminti a duk shekara, kuma kamfanin da ake da shi na Ibeshe, yana samar da metric ton miliyan 12, don haka samar da siminti a jihar zai kai metric ton miliyan 18 a duk shekara, wanda zai zama mafi girma a samar da siminti a Nijeriya da kuma yankin Sahara.
Gwamnan ya yaba wa kamfanin bisa yadda bai yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da ayyukan da suka dace na hadin gwiwa a tsakanin al’umma, kamar yadda a halin yanzu yake aikin gina titin ‘Inter-Change-Papalato-Ilaro’, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta hada kai da kamfanin domin ci gaban jihar da kasa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp