Kwamishinan ƴansanda, CP Miller Dantawaye, ya karɓi ragamar aiki a ranar Juma’a a matsayin kwamishina na 34 na hukumar ƴansanda ta babban birnin tarayya (FCT). Hakan na zuwa ne bayan sauya sheƙa da aka yi wa tsohon kwamishina, CP Ajao Adewale, sakamakon jerin hare-haren fashi da makami da suka faru kwanan nan a Abuja.
Kakakin hukumar ƴansanda ta FCT, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da fara aikin sabon kwamishina, inda ta bayyana cewa CP Dantawaye ya gaji Adewale wanda aka mayar zuwa wani muƙamin a ofishin babban sufeton ƴansanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun. Ta ce Dantawaye gogaggen jami’in tsaro ne mai fiye da shekaru 20 yana aiki da kwarewa a fannoni daban-daban.
- Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja
- ‘Yansanda Sun Ceto Wani Dan Shekara 25 Da Aka Sace A Jihar Kebbi
An haifi Dantawaye a ranar 15 ga Oktoba, 1971 a Afogo, ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna. Ya yi karatunsa a makarantun firamare da sakandare a Kwara, da Katsina da Enugu, kafin ya ci gaba da karatun digiri a fannin nazarin ƙasa da ƙasa a jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, da kuma digirin digirgir a jami’ar Ilorin. Ya shiga aikin ƴansanda a matsayin Cadet ASP a shekara ta 2000, inda ya fara aiki a jihar Bayelsa bayan kammala horo.
A cikin shekaru da dama da ya shafe a aikin tsaro, CP Dantawaye ya riƙe muhimman muƙamai a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da mai kula da harkokin aikata laifuka a Yenagoa, ADC ga tsohon gwamnan Bayelsa, shugaban MOPOL 24 a Villa, da kwamandan motocin rakiyar shugaban ƙasa. Haka kuma, ya kasance ACP a Abuja, DCP a jihohin Edo da Yobe, sannan kafin wannan naɗin, shi ne kwamishinan ƴansanda na Jihar Kogi.
CP Dantawaye ya halarci kwasa-kwasai da dama a cikin gida da ƙetare, ciki har da horon yaƙi da ta’addanci a Gwoza, da horon jagoranci a Jos, da kwas a fannin tsaron manyan baki a Isra’ila. Haka kuma, yana da nasaba da cibiyoyin ƙwararru kamar NIPR da Rotary International, inda ake girmama shi saboda jajircewa da kishin aiki.
Abin da ya rage yanzu shi ne za a zuba ido don ganin irin sauyin da zai kawo na tsaro a birnin tarayyar, sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ya addinin garin.