Jimilar darajar kayayyakin da Sin ta fitar ketare da wanda suka shigo kasar daga ketare, ta karu da kaso 0.03% a bana, zuwa yuan triliyan 34.32, kwatankwacin dala triliyan 4.78, cikin watanni 10 na farkon bana.
A cewar hukumar Kwastam ta kasar, darajar kayayyakin da ake fitarwa ketare ya karu da kaso 0.4% kwatankwacin na makamancin lokacin bara, zuwa yuan triliyan 19.55, yayin da darajar kayayyakin da ake shigowa da su kasar, ta ragu da kaso 0.5%, zuwa yuan triliyan 14.77.
Cikin watan Oktoba kadai, darajar cinikayyar Sin a ketare ta karu da kaso 0.9% daga shekarar da ta gabata, zuwa yuan triliyan 3.54. (Fa’iza Mustapha)