Darajar kasuwar kayan aikin likitancin kasar Sin ta kai kudin Sin RMB yuan triliyan 1.35, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 188.2 a shekarar 2024, a cewar wani taron kayayyakin aikin likitanci da aka bude a yankin Chongqing da ke kudu maso yammacin kasar Sin jiya Asabar.
Mataimakin ministan masana’antu da sadarwa na kasar Sin Xin Guobin ya ce, kasuwar mai kyakkyawar makoma har yanzu tana kara habaka, inda a shekarar 2024, yawan kudaden shiga da manyan masana’antun samar da kayan aikin likitanci na kasar Sin suka samu ya zarce yuan biliyan 540, wanda ya ci gaba da bunkasa cikin sauri kusan shekaru goma.
- Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ya Shaida Yunkurin Lai Ching-te Na Neman Mulki Irin Na Kama Karya Ta Hanyar Demokuradiyya
- Fitar Da Nama Zuwa Saudiyya: Mayankar Dabbobi Ta Jurassic Ta Yi Hadin-gwiwa Da Shirin CDI
A kasar Sin, manyan kamfanonin masana’antu suna nufin wadanda ke samun kudaden shiga na shekara-shekara da yawansu ya kai yuan miliyan 20 ko fiye da haka.
A sa’i daya kuma, madam Qiao Jie, masaniya a kwalejin injiniya na kasar Sin, ta yi kira da a yi kokarin karfafa yin kirkire-kirkire a masana’antun, da sa kaimi ga hada kayan aikin likitanci tare da fasahar kirkirarriyar basira AI, da kara kyautata kayayyakin kasar Sin a kasuwannin ketare. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp