Naira ta sake faduwa wanwar a kan Dala a jiya Laraba a kasuwar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki, inda aka yi musanya a kan N426.58.
Adadin ya nuna faduwar darajar Nairar da kashi 0.57 idan aka kwatanta da N424.17 da aka yi hada-hada da Dala a ranar Talata.
- Gwamnatin Zamfara Ta Hana Nadin Sarauta A Fadin JiharÂ
- INEC Ta Mayar Wa Davido Martani Kan Bai Wa Adeleke Takardar Shaidar Lashe Zabe
Hada-hadar ta rufe ne a kan bayyanannen farashi na N426.50 a Dala a jiya Laraba.
Canjin N444 zuwa Dala shi ne mafi girman farashin da aka samu a cinikin yau kafin ya daidaita a kan N426.58.
Ana siyar da Naira a kan N414 ga Dala a kasuwar ranar.
An yi cinikin Dala miliyan 144.03 a musayar kudaden waje a kasuwar masu saka hannun jari da masu fitar da kayayyaki a jiya Laraba.