A kalla daraktoci biyu da wasu jami’ai biyar na sashin kula da filaye na hukumar bunkasa babban birnin tarayya (FCDA) da sashin kula da harkokin cigaba (DDC) na fuskantar tuhume-tuhume a gaban ‘yansanda kan zarginsu da ake yi da tafka badakar fili.Â
A cewar ‘yansandan, za a gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kotu nan ba da jimawa ba.
Wannan matakin na zuwa ne a dai-dai lokacin da sabon ministan babban birnin tarayya Mista Nyesom Wike ya sha alwashin dakile duk wata harkar filaye ta barauniyar hanya a kokarinsa na kwato asalin taswirar birnin tarayya.
Tuhume-tuhumen da ‘yansanda ke musu sun hada da aikata babban laifi, amfani da takardar bogi, karya da kuma sojan gona.
Wannan lamarin ya sanya ‘yansanda kaddamar da bincike kan takaddamar waye hakikanin mamallakin fili a tsakanin kamfanin ‘Cona Engineering and Technical Services Nigeria Limited’ da kuma wani Yusuf Daniel Ogwu kan filin da ke lamba 1308 Cadastral Zone A09 a gundumar Guzape, Abuja.
Kamfanin ta tura ma’aikata domin su fara aikin gini a filin kafin shi Yusuf Daniel Ogwu ya ankare tare da gabatar da shaidar R of O da ke ikirarin shi ne hakikanin mamallakin filin.
Sai dai kuma takardun da ke akwai sun nuna cewa takardar shaidar mallaka COG an mallaka wurin ne ga Jamila Saleh Hassan a ranar 6 ga watan Yunin 2007 (file No: 20400), da ta kasance mai cin gajiya kuma mamallakiyar filin mai lamba 1308 Cadastral Zone A09 gundumar Guzape, Abuja.
Jamila Saleh Hassan, ta kyautar da wurin ga wani Sunday Benjamin Egele a wani watan Yunin 2014.
Kazalika, shi ma Sunday Benjamin Egele ya kyautar da wurin ga kamfanin Cona Engineering and Technical Services Limited, a watan Disamban 2018.