Kwanakin baya Gidan Talabijin na Kausain TB wanda yake daya daga cikin rukunin kamfanonin Kauisain ya bayyana wasu sabbin nade naden da ya yi domin su jagoranci kamfanin a bangarori da dama, a cikin sanarwar Kausain TB ta ce ta nada fitaccen jarumin fina-finan Kannywood kuma mawaki Adam A. Zango a matsayin Darakta Janar na gidan Talabijin din.
Shugaban kungiyar Kausain, Alh Nasir Idris, a wata sanarwa a ranar a Abuja, ya bayyana cewa nadin Adam Zango a matsayin Darakta Janar ya fara aiki nan take, a cewar sanarwar an amince da nadin ne yayin wani taron kwamitin gudanarwar kamfanin da aka gudanar.
- Gyaran Mama Ga Matan Da Suka Haihu
- An Gudanar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomi Cikin Kwanciyar Hankali A Kaduna – Gwamna Sani
Malam Idris ya kara da cewa an nada tsohon Gwamnan Soja na Jihar Kano, Kanar Sani Bello (mai ritaya) a matsayin Shugaban Amintattun kamfanin, ya kuma ce an nada tsohon ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital, Farfesa Isa Pantami a matsayin Darakta mai zaman kansa, sai kuma nadin da aka yiwa tsohon mai watsa shirye-shiryen sashen Hausa na BBC, Ahmad Abdullahi a matsayin Darakta mara zartarwa.
Ya ce nadin nasu ya zo ne bayan dogon nazari da hangen nesa ta inda ake fatan dukkansu za su hada kai wajen bayar da shawarwarin da suka dace wajen ciyar da kamfani gaba duba da cewa dukkansu kwararru ne a wannan harka.
Ayyukansa sun hada tsare tsare ga Kausain TB, samar da sabbin dabaru wajen gudanar da kamfani da kuma kawo sauye sauye a bangaren tallace tallace na kamfani inji shi.
Ya bukaci wadanda aka nada da su yi amfani da kwarewarsu wajen ciyar da kamfanin gaba inda ya ce, muna da tabbacin cewa kwarewarku da zurfin fahimtar ku za su taimaka wajen ciyar da kamfanin gaba da kuma samun manyan nasarori in ji shi.
Nan take bayan wannan sanarwar jarumi Adam Zango kuma sabon Darakta Janar na Kausain TB ya wallafa a shafinsa na Facebook domin yan uwa da abokan arziki su taya shi murna akan wannan sabon mukami da ya samu, daga cikin wadanda suka taya shi murna akwai shugaban hukumar Fina Finai ta Nijeriya Ali Nuhu Muhammad wanda ya yi mashi fatan alheri da addu’ar samun nasara.