‘Yan’uwa Musulmi assalamu alaikum warahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Barkan mu da Juma’a, da fatan Allah ya karbe mu da falalarsa. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata mun tsaya ne a kan yadda Shehu Ibrahim (RA) ya hori almajiransa da su dinga yin saukar Alkur’ani a cikin Sallar Tarawihi lokacin Azumin Ramadhan. A wajen almajiran Shehu aka fara ganin haka a Kaulaha.
Sannan ya karfafa yin haddar Alkur’ani maigirma. Albarkar Shehu da kafa makarantun da ya yi, an samu sauki sosai wajen yin haddar Alkur’ani. Bayan haka, Shehu (RA) ya koya mana ‘yancin zabi a cikin addini ta yadda kowa zai bi hanyar da yake ganin zai tsira.
- Darussa Daga Rayuwar Shehu Ibrahim Inyass (RA) Wajen Yada Musulunci
- Samar Da Jami’ar Musulunci A Jihar Kaduna Alheri Ne – Bola Ige
Shehu Ibrahim (RA) ya taimaki addini da kayan zamaninsa da ya tarar wanda Turawan mulkin mallaka suka yi amfani da su. Shi ne farkon Musulmin da ya yi haka. Ya yi amfani da Rediyo, da Tarho, da Rikoda, da Kamara wajen isar da sakon Musulunci. Don har yau, akwai gidahumin musulmin da yake ganin yin hoto kafirci ne, amma Shehu Ibrahim ne ya wayar mana da kai a kan amfani da wadannan kayan a cikin addininmu na Musulunci. Haka nan amfani da motoci da jirgin sama, da lasifika, da agogo, da zuwa asibitoci.
Shehu Ibrahim yana daga cikin wadanda ya tilasta wa almajiransa zuwa asibiti wanda a da ba a yarda da hakan ba. Sannan ya koyar da yin karatu irin wannan da ake yi na zamani a makarantu.
Shehu Ibrahim (RA) shi ne farkon Musulmi kuma Malami da ya waye ya san cewa “technology” ba kishiyar addini ba ne. Shi ne farkon malamin da ya yarda cewa Turawa sun je duniyar wata a shekarar 1969 (combo apolo 11) har ma ya yi littafi a kan wannan. Kuma ya yi wa shugaban Amurka na lokacin wasika a kan wannan (documents suna nan a kan haka). Su Malaman Saudiyya cewa suka yi ma duk wanda ya yarda cewa an je duniyar watan kafiri ne, su kuma na Azahar (Misra) suka ce sam ma ba zai yiwu ba. Amma Shehu Ibrahim ne ya gamsar da su (da hujja) har suka yarda da abin.
Shehu Ibrahim (RA) ya kewaya kasashen duniya har Chana, Beijin, Honkon, da sauran sassan karshen Asiya don taimakon Musulunci. Ya hada kan Musulmi Larabawa da Bakar Fata. Yana da kishi na hakika a kan addininsa na Musulunci mai tsafta ba na ta’addanci ba.
Shehu Ibrahim (RA) yana da kishi a kan Afirka. Ya yi tsayuwar daka tare da ba da gudummawa ga samun ‘yancin duk wata kasa ta Afirka ciki har da kasarmu Nijeriya. Yana da kishin mutane bakar fata ‘yan’uwansa.
Bayan haka, Shehu Ibrahim (RA) ne gwarzon namijin da ya tsaya shi kadai ya kori Isra’ila daga kasarsa Senigal wanda nan ne hanyar shigowa Afirka. A lokacin, Faransa ta yiwa Yahudawa izinin shiga Afirka ta Senigal ba tare da takardar biza ba ma. Ba domin Shehu Ibrahim ya kore su ba da mu ma yanzu abin da yake samun Palasdinawa ya same mu. Jamilu Arif, wani danjarida na kasar Misra ya fadi wannan.”
Da yake duniya ta bunkasa da kakkafa kungiyoyi don cimma abubuwa da dama da aka tasa a gaba, Sayyid Isma’il Maidiwani ya yi bayanin cewa Shehu Ibrahim ya ba da gudummawa ta wannan fuskar don ci gaban Musulunci.
Shehu (RA) ya ba da gagarumar gudummawa wajen kafa Rabida ta Malaman Musulunci na Duniya (duk akwai hujjoji a kai a hannu). Sannan ya kafa hadin kan Afirka wanda ta hannunsa ne shugabannin Afirka suka karbi wannan. Ya kuma kafa kungiyoyin da za su taimaki addini irin su Ansarid Dini tare da umurtar almajiransa su kafa, mu nan a Nijeriya akwai Fityanul Islam.
Manyan ‘yanjarida na duniya Turawa da Larabawa da sauran su duk sun yi magana a kan Shehu Ibrahim (RA). Ustazu Abdulkareemin Niyazi ya yi magana a kan Shehu da irin kokarinsa a Jaridar Saudiyya. Haka nan Jamilu Arif na Misra ya yi magana a kan Shehu. Sannan babban malamin Saudiyya Sheikh Muhammad Mahmud Sauwaf a cikin littafin da ya yi mai suna “Yawona Zuwa Kasashen Musulunci” ya yi magana a kan Shehu (RA).
Shehu Ibrahim ne malami bakar fata da ya samu daukakar yiwa Musulmi Sallar Jumma’a a Jami’ar Az’har ta Misra a 1961, wanda kafin shi ba a taba yin wannan ba (RA).
Haka nan ya rike mukamai da yawa a duniya. Shehu ne na Musulunci wanda yake da fahimtoci a cikin Tauhidi, ya warware abubuwan da ya gagari malamai a cikin Tauhidi cikin sauki. Daga cikin mukaman da ya rike a duniya akwai shugaban hadin kan Jami’ar Kairawani da Jami’ar Az’har. Sannan ya rike mataimakin taron Musulunci da aka yi a Karachi ta Pakistan. Yana daga cikin kwamitin da ya kafa Rabida ta Malaman Musulunci na duniya a Makka. Sannan yana cikin kwamitin da ya hada kan jami’o’in Musulunci na duniya a Ribad na Moroko. Haka nan yana daga cikin babban kwamitin malamai masu yiwa abubuwa hukunci a Musulunci na Misra. Ya rike babban matsayi a taron shekara-shekara na bincike a cikin Musulunci a Misra. Har ila yau, yana da matsayi babba a Majalisar Musulunci ta Jaza’ir da sauran su da dama.
Shehu Ibrahim (RA) ya ci nasara wajen yin kira zuwa shiga addinin Musulunci da hikima da wa’azi mai kyau da jayayya mafi kyau. Idan muka ce Musulunci ma’ana ya hada da Musuluncin, da Imani da Ihsani kamar yadda Hadisin Annabi (SAW) ya fada a Hadisin Jibrilu. Ba a dinga daukar bangaren Fikhun addini kadai a bar sauran ba kamar yadda ta ke faruwa a wannan zamanin, sai mutum ya hada duk gaba daya. Amma idan mutum ba zai iya hadawa ba, ya tsaya wa Fikhun addini na makamul Islam din kawai amma kuma ya san cewa akwai karatun Imani na ilmud Tauhidi ba adadi a gabansa da bai sani ba, ballantana kuma ilmut Tasawwuf na Ihsani.
Babban makaminsa na wannan aikin shi ne tsoron Allah, da ilmi sannan ya fahimci zamaninsa (wannan nukuda ce babba). A takaice dai kowa ya tabbatar ba a taba yin Gwarzon Namiji a Musulunci ba irin Shehu Ibrahim (RA) a karne na 20, ba mu Afirka ba har da kasashen Larabawa. Ya bunkasa ilmin addini da Luggar Larabci a Afirka wanda duk ga ‘yan jami’a nan suna ta amfani da karatuttukansa. Bayan wannan, ya watsa ‘ya’ya da jikokinsa da almajiransa a kasashen Turai suna musuluntar da su tare da karantar da su. Tun komawarsa ga Allah har yau; har abada duk wani abu mai amfani za ka ga imma dai ‘ya’yansa ko jikoki ko almajiransa ne suke jagoranci a kai.
Shehu ya kafa alheri, ya yada alherin amma sai aka zo da kishiyarsa, zuwa da kishiyoyinshi abubuwan da ya kafa ne ya kai Afirka cikin bala’in da ake ciki. Amma yanzu da yake an ce ana so a gyara, to lallai a dawo da wannan alheri da kwarewa da cin nasarar da Shehu ya yi, idan aka yi haka da albarkar Annabi (SAW) sai a samu nasarar da ake bukata.
Rikicin wadanda ba su fahimci Shehu Ibrahim Inyass ba kawai ya ta’allaka ne a kan kin tsayawa a matakin ilimin da suke da shi, inda suke kutsawa cikin fannoni ko matakan addini da ba su san komai a kai ba, “suna matakin Fikhun Musulunci amma sai su rika tsallakawa Matakin Imani na Tauhidi ko Ihsani na Sufanci su rika cewa “ya fadi kaza a wuri kaza” alhali ba su da ilmi a kai kwarai da gaske.
Da kowa zai yi adalci ya tsaya a fanninsa sannan ya dauki karatun da Shehu Ibrahim ya yi a kan wannan fannin, da ya san Shehu Shehinsa ne don ya karantar da shi a fannin nasa ma. Haka nan Shehu Ibrahim ya kawar mana da kabilanci a tsakaninmu tare da yaukaka zumunci na ‘yan’uwantaka wanda hatta makiyinsa ma ya yi ma sa shaida a kan wannan. Ko a kan haka, ya dace kwarai da gaske mu rika yin Mauludin Shehu Ibrahim (RA).