Assalamu alaikum wa rahmtullah. Masu karatu barkanmu da war haka, barkanmu da sake saduwa a wani makon a filinmu na Dausayin Musulunci.
A wannan makon ma, za mu ci gaba da kawo darussan tafsirin Alkur’ani mai girma da muka samu sakonninsu daga masu bibiyar karatun, kamar yadda muka faro a makonni biyu da suka gabata. Ga sakonnin na wannan karon kamar haka:
- Hakuri Da Baiwa (Kyautar) Manzon Allah (SAW)
- Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
•Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni
Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Shehu Malam Isma’ila Mai Diwani da sauran jama’arka ta Ahlul Faidhati Mai Diwani Group, da fatan kuna nan cikin koshin lafiya. Sakona shi ne ina so na yi tsokaci ne a game da tafsirin da ka gabatar a rana ta 10 na Azumin Ramadan da ya gabata inda ka yi yi bayani a game da cewa, Shari’ar Manzon Allah (SAW) ta zo da wayewa ta rayuwar duniya a ko wane fanni, wanda hakan yake kara nuna gaskiyarta a aikace a harkokin rayuwa na kasashen da suka ci gaba a duniya.
Lallai duk tsare-tsaren da ake gani na kiyaye rayuka da nuna gaskiya da adalci baki daya wayewa ce ta Shari’ar Manzon Allah (SAW) kuma ba dole sai a tsakanin musulmi ba saboda dukkan ‘yan Adam da ke rayuwa a doron kasa yanzu suna cikin al’ummar Annabi (SAW) kuma haka Allah ya halicce su a kai tun asali na Fidira. Koyarwar da Annabi (SAW) ya yi a aikace game da yanke hukunce-hukunce na haddi wanda karshen sauki yake dauka ya nuna mana irin rahamar da shari’arsa ta zo da ita, kamar yadda Allah ya sa ka’idoji masu tsauri da dole a tabbatar kafin yanke hukunci mai tsanani.
Matakan hukunci na Shari’ar Manzon Allah (SAW) na farawa ne daga Yafiya, sai Biyan Fansa, daga nan sai tasa keyar mai laifi zuwa Gidan Gyaran Hali (Kurkuku), kuma abu na karshen shi ne Kisa. Idan aka kama mai laifi aka kai shi gidan gyaran hali, an yanke shi daga zuwa wani wuri balle ya je ya aikata laifi, don haka ba manufar Musulunci ba ne ya sa a yi ta yanke wa mutane hannu ba kamar yadda wasu malamai suke ta fada. Manufar Musulunci ita ce a gyara al’umma amma ba a yi mata tsanani ba wanda hakan ya sa Allah ya kafa matakai masu tsauri na kawo shaidu a kan haddi.
Hakika, duk tsanance-tsanance na kisa da ake gani a wasu littafai na fikihu an shigo da su ne a zamanin mulkin Umayyawa da Abbasawa saboda siyasa amma asalin abin da yake a Musulunci shi ne, Annabi (SAW) ya ce a dinga yasar da haddi da shubuha, ma’ana a rika neman yin haddi da karshen sauki, kamar yadda ake yi a wasu kasashen duniya, domin Shari’ar Manzon Allah (SAW) ta duk duniya ce “International”.
Kuma ayoyin da ake maganar jihadi a kai ba na kashe-kashen rayuka ba ne, don kalmar “kitalu” ce take daukar ma’anar amfani da makami amma ba ta jihadi ba. Kuma Musulunci ba ya tilasta wa mutane shiga addini, don haka yaki sai idan ya zama zabi na karshe shi ma saboda maslaha sai a gwabza amma ba don kisa ba kawai.
Allah ya saka da alheri da wadannan darussa da muke koya daga tafsirinka na Ramadan, ya Shehu. Godiya mai yawa.
Sako daga Mustapha Usman
•Tsarin Mulki Na Zamantakewa (Constitution) Ya Samo Asali Ne Daga Annabi (SAW)
Salamullahi alaikum, ya Shehi muna muku barka da wannan lokaci, da fatan kuna nan cikin koshin lafiya. Allah ya saka muku da alkhairi bisa irin yadda kuke kara wayar mana da kai game da rayuwarmu ta musulunci.
Alhamdu lillah, ni daga babban abin da na fa’idantu da shi a Tafsirinka na bana shi ne yadda tsarin Mulki na constitution ya samo asali daga Annabi (SAW) lokacin da ya isa Madina bayan Hijira. Tabbas Wasikatu Madina da ka yi magana a kai wanda Annabi (SAW) ya tsara, tana nuna wa al’ummar musulmi wayewa ta zama da mutanen da ba addininsu daya ba cikin zaman kafiya da kwanciyar hankali da kuma kyakkyawar mu’amala.
Bugu da kari, yadda shi ma Sayyadina Abubakar ya tsara nasa daban saboda la’akari da zamaninsa da yadda Sayyadina Umar shi ma ya yi nasa, haka nan Sayyadina Usman har zuwa kan Sayyadina Ali wanda shi ma ya tsara nasa, duk suna nuna wa al’ummar musulmi ne cewa tsara constitution ba abu ne na kafirci ba, yana da asali a Musulunci. Kuma har ila yau, yana nuna yadda musulmi suka fara kawo wayewa ta zaman tare domin maslaha da ci gaban al’umma. Sannan ba a tsaya a kan guda daya ba, yadda Annabi (SAW) ya yi nasa da sauran dukkan manyan Sahabban kowa ya yi nashi tsarin daban, yana nuna wa ko wace al’umma ta yi la’akari da zamaninta ta tsara nata bisa maslahar al’umma.
Har ila yau, muna godiya da kuma jaddada kiran da ka yi ga sauran Malaman Musulunci da su rika kira da irin fahimtar zamani domin tafiya da asalin tushen ci gaba na zamani wanda ake amfani da shi a duk duniya a yanzu har mu zama mun wayi gari dai Afirka musamman Nijeriya ta yi kafada-da-kafada da Amurka a fannin ci gaba, har ma a kai ga mun wuce ta ma.
Tabbas, wadannan kasashe ba su fi Afirka da komai ba, abin takaici ma shi ne su da ake ganin ba musulmi ba ne sai ya zama suna amfani da wayewar cikin Alkur’ani wajen karatuttukansu da gudanar da harkokinsu wanda mu ne muka fi dacewa mu yi hakan. Domin irin kundayen karatuttuka da suka tanada misali kamar a Congress ta Amurka da dakin karatu na Ingila da Bertican, ko Makka da aka saukar da Alkur’ani a ciki ba ta da su, kuma wannan babban kalubale ne ga ci gaban musulmi da musulunci a wannan zamanin. Wallahi ya kamata duk Musulmi a ko ina cikin duniya na zamanin nan mu farka.
Allah ya saka muku da alkhairi. Muna godiya sosai, Allah ya kara Faila a yi ta kwaranyo mana ilimi da hikimomi da karin madadi mai yawa.
Sako daga Sayyadi Mushri Nuhu (Matasan Faila)
•Batun Tsarin Aurarraki A Cikin Addinai
Assalamu alaikum. Akramakallah, bayan gaisuwa da salati ga Shugaban Halitta, Manzon Rahama, Annabi (SAW) da Alayensa da Sahabbansa, ina mika ziyara da kuma gaisuwa ta musamman da jinjina a kan yadda ka yi mana bayani dalla-dalla game da tsarin aure a cikin addinai da Allah ya saukar da kuma yadda yake a tsari na rayuwar mutane da aka amince da shi.
Ni a baya, nakan yi tunanin yadda wadanda ba musulmi ba suke yin aure a tsakaninsu saboda ban taba zuwa ko daya ba, amma sakamakon karatukan da na ji na fahimci irin alkawarin da auren addinin Kirista ya kunsa da sharuddan auren addinin Yahudanci da kuma yadda Allah Ta’ala ya yi gyara a kai ya zama a cikin shari’ar Musulunci ta Annabi (SAW).
Haka nan mun samu karin haske bisa bayanin da ka yi a kan tsarin aure na kotu da kuma wanda mutanen gari suka amince da shi, da ka’idoji da dokokin yin saki da komawa da mata bayan saki da kuma iddar da ake yi.
Hakika, mu musulmi ya kamata mu fahimci yadda addinin Musulunci ya yi tanade-tanade masu sauki na gudanar da aure kuma mu yi aiki da su ba kamar yadda wasu suke tsanantawa ba musamman ma a bangaren malamai, domin haka duk wani malami da zai kawo mana tsanani har ma ya fi na yadda yake a sauran addinai to ya kamata a watsar masa da kayansa, domin ya saba da asalin yadda shari’ar Annabi (SAW) ta shimfida.
Kuma muna addu’a, Allah ya saka da alheri dangane da cikakken bayanin da ka yi mana mai gamsarwa a kan sharuddan aure da saduwa da wata mace wadda ba a karkashin kulawar kowa take ba, da ka’idojin kiyaye hakkinta da kuma halascin mallakar da ko ‘yar da za ta haifa. A bisa wannan, musulunci ya kawo mana saukakan hanyoyi na gudanar da rayuwa, amma wasu ne suka shigo mana da tsanance-tsanance da muke gani wanda ya kamata mu gyara tsakani da Allah.
Kuma kiran da ka yi ga maza da ke son sakin matansu a kan su rika bin ka’idojin da shari’a ta asali ta gindaya da kyautata wa matar da za a saka abu ne da ya kamata gwamnati musamman na jihohinmu na arewa da suka ce sun kaddamar da shari’ar Musulunci su rika tilastawa ba a bar shi a matsayin zabi ko ganin dama ba kawai. Idan har za mu yi haka, za a rage mace-macen aure da yawa, sannan za a kawar da tsananin damuwa da ake jefa mata a ciki.
Akramakallah, darussan da ka koyar da mu a game da asalin aure da alkawarin da yake ciki da hakkokin da suka kamata a kiyaye ga kowane bangare na ma’auratan, a karatunka na tafsirin rana ta tara (9) karatu ne da ya kamata a rubuta a matsayin littafi guda. Allah ya saka da alheri.
Bugu da kari, mun karu da sharhin da ka yi da tarihin da ka bayar a kan farkon soke bautar da bayi da ‘yanta su a duniya tun daga 1807 daga kasar Birtaniya har zuwa 1949 da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, da kuma kawo karshen lamarin baki daya a 1964 wanda Sarki Faisal na Makka ya tabbatar a daular Saudiyya.
Mun gode da wadannan karatuttuka, Akramakallah. Allah ya kara ilimi da fahimta, ya kuma yawaita mana irinku a cikin al’ummar musulmi, amin.
Sako daga Nuruddeen Shamsu Katsina
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp