ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, June 21, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hakuri Da Baiwa (Kyautar) Manzon Allah (SAW)

by Dausayin Musulunci
1 year ago
Allah

Dukkan kabilar kuraishawa sun yi tsammanin Annabi (SAW) zai karar da kabilarsu ne gaba daya a lokacin Fat’hu Makkah, sai ya ce musu “me kuke tsammani daga gare ni?”, sai suka ce masa “kai dan’uwa ne mai karamci kuma dan dan’uwa mai girma”, sai ya yafe musu ya yi musu irin ta Annabi Yusufa da ‘yan uwansa, “la tasriba alaikumul yauma…” an yafe muku, babu wani zargi a gare ku.

Sayyadin Anas, ya ce, yayin da Annabi (SAW) ya yi nufin zuwa Umra bayan yakin Badr, ya isa Hudaibiyya, sai samarin Makkah su 80 suka kawo masa hari cikin dare amma ba su yi nasara ba duk an cafke su, Annabi (SAW) ya ‘yantasu duka duk da cewa sun yi nufin kashe shi ne. Sabida haka, sai Allah ya saukar da aya yana cewa “wahuwallazi  kaffa aidiyahum ankum wa aidiyakum anhum bi badni makkata min ba’adi an azfarakum alaihim,wa kanallahu bima ta’amaluna basira” Allah shi ne wanda ya rike hannayensu a gareku (ba za su iya cutar da ku ba) kuma ya rike hannunku a gare su (ba ku karkashe su ba) yayin da ya dora ku a kansu, Allah masani ne a kan duk abin da kuke shiryawa.

  • Wasu Ruwayoyi Game Da Yafiyar Manzon Allah (SAW)
  • Na Rantse Da Allah Binani Ce Ta Lashe Zaɓen Gwamnan Adamawa A 2023 – Tsohon Kwamishinan Zaɓe

Manzon Allah ya fada wa Abu Sufyan (sirikinsa ne kuma kwamandan yaki da ya dinga shiryo wa Annabi (SAW) yaki kuma shugaban cutar da Annabi (SAW) lokacin ana zaman Makkah) yayin da aka kama shi a yakin Fat’hu Makkah, “kaiconka, kai har yanzun ba ka yarda Allah shi ne daya ba kuma ni Manzonsa ne?”, cikin taushin magana Annabi ya fada masa, sai Abi Sufyan ya ce “na ba da iyayena fansa a gareka, mamakin irin taushin zuciya da hakurinka da sada zumuncinka da karamcinka, yau ranar ramuwa ce amma duk ka nuna wadannan kyawawan halayen.”

ADVERTISEMENT

Amma in mun sauya akalar karatunmu zuwa ‘Baiwar Annabi (SAW)’ za mu ga babu wani kamarsa.

Baiwa ana fassarta da ciyarwa ko kyauta da tsururi ko barin hanyar da a karshenta za a yi da-na-sani ko kuma za ta iya zubar da darajar Mutum. Ma’ana, baiwa ita ce kyauta.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

Annabi (SAW) a cikin dukkan kyawawan halaye ba a kamanta shi da kowa.

Jabir dan Abdullahi (RA) yana cewa, ba a tava tambayar Annabi (SAW) da wani abu ba ya ce babu.

Abdullahi dan Abbas (RA) yana cewa “Annabi (SAW) ya kasance mafi baiwar Mutane da alkairi, lokacin da Annabi ya fi baiwa, shi ne lokacin watan Azumin Ramadana, ya kasance idan ya hadu da Mala’ika Jibrilu, Mala’ika Jibrilu yana zuwa suna Musaffan Karatun Alkur’ani da Annabi (SAW) duk watan Ramadana sau daya, sai shekarar wafati ce suka yi sau biyu.

Shi ya sa, duk musulmai suna da baiwa da kyauta amma in watan Ramadana ya zo sai ka ga sun kara ninkawa.

An karvo hadisi daga Anas khadimin Manzon Allah (SAW) ya ce, wani Mutum ya nemi kyauta daga Manzon Alla (SAW), sai ya ba shi Tumaki tsakanin duwatsu biyu cike da dabbobi amma Annabi sai da ya ba shi dukkansu (SAW). Wanann ya faru ne a lokacin yakin Hunaini, Sahabin shi ne Safwan bin Umayya. Annabi ya gan shi yana ta kallon tumakin, sai ya tambaye shi, sun burge ka ne? sai ya ce Ya Rasulallahi wane Balarabe ne zai ce bai son wannan, take Annabi ya ce masa ya dau sanda ya kora su ya bar masa. Sai Safwan ya koma wurin mutanensa ya ce musu ku Musulunta sabida ‘Muhammad’ (SAW) yana bayar da kyauta irin wacce ba ya tsoron talauci.

 

Wata rana Manzon Allah (SAW) ya bai wa Abu Sufyan Rakumi 100 a lokaci daya, ya bayar da dukiya mai yawa da ba a san adadinta ba da aka samo ganima a yakin Hunaini.

Yakin Hunaini, yaki ne da ya kasance bayan fitowar Annabi (SAW) da rundunar yaki sama da 10,000 don bude Makkah, amma kuma sarkin Hunain ya karya alkawari da Annabi (SAW), ya ji labarin rundunar da Annabi (SAW) ya fito da ita, sai ya tara ninkin ta Annabi Uku (30,000) kuma ya ce kowannensu ya fito da duk dukiyar da ya mallaka da kuma iyalansa (Mata da Yara), rundunar Hunaini dukkansu maharba ne. Bayan Annabi (SAW) ya bude Makkah, ya samu karin mayaka, sai ya nufi Hunaini, wasu daga cikin Sahabbai suka fara alfahari cewa “Yau babu wata runduna da za ta iya kayar da mu”, bayan Annabi ya fada wani kwari a hanyar zuwa Hunaini, ashe duk rundunar maharba su 30,000 suna sama kowanne da kibiya a hannu, kawai sai suka yo ruwan kibiyoyi ga sahabbai, nan fa kowa ya arta a guje sai Mutum 100 kacal, Annabi (SAW) ya watsa musu kasa duk ta cike idanuwan maharban sannan ya sa Baffansa Abbas ya kira Mutanen Madina. Allah ya ba wa Annabi (SAW) da rundunarsa Nasara, Kafirai sun bar dukiyoyinsu da Iyalansu.

 

Wannan dukiya da suka bari mai yawa, Annabi (SAW) ya jira ko za su dawo su Musulunta ya mayar musu da dukiyarsu amma ba su dawo a lokaci ba har sai da Annabi (SAW) ya rabar da dukiyar baki daya sannan suka dawo.

Annabi (SAW) ya nemi zabinsu a kan wanda ya fi, muhimmanci a wurinsu, Dukiyarsu ko Iyalansu, sai suka zavi Iyalansu, an ce Annabi ya maida musu da ‘yan mata sama da 6,000.

Annabi (SAW) ya ba wa baffansa Abbas dukiya (zinare) ya dauka iya karfinshi, an kawo wa Annabi (SAW) daga ganimar yakin kudi Dirhami 90,000, Annabi (SAW) ya sa aka shimfida tabarma a Masallaci, har sai da ya rabar da kudin gaba daya, Abbas ya ce ya dana a yakin Badr sai da kasa na biya fansar Mutum Uku, kai ka maida ni Talaka don haka yanzu ga kudi a maida min da kudina, shi ne Annabi (SAW) ya hore shi da ya diba zinare iya karfinshi. Bayan an gama rabo sai wani ya zo ya ce Ya Rasulallahi ina nawa? Annabi ya ce masa komai ya kare amma ya je ya ci bashi zai biya masa in an samu kudi. Sai Sayyadina Umar ya ce Ya Rasulallahi Allah bai dora maka abin da ba zaka iya ba, Annabi (SAW) ya ki wannan maganar, sai wani daga cikin Sahabbai ya ce Ya Rasulallahi ka ciyar, kar ka ji tsoron wani talauci daga Ubangjin Al’arshi, sai Annabi (SAW) ya yi farin ciki kuma aka ga bishara a fuskarsa.

An karvo daga Mu’awwizu bin Afra’a (Sadaukin Badr) yana cewa, wata rana na zo wurin Annabi (SAW) ina dauke da faifai da Dabino a kai, hakikanin Hadisin ‘yarshi ce ya aiko ba shi ne ya zo da kanshi ba, ta ce na zo wurin Annabi (SAW) da faifai akwai Dabino danye da Vuluvutu danye wanda bai girma sosai ba a kanshi, sai Annabi (SAW) ya ciko hannunsa da kayan kwalliya na Mata (Awarwaro) na zinari ya ba ni.

Khadiminsa Anas, ya kasance yana cewa, Annabi (SAW) ba ya ajiye komai sabida gobe a kan-kansa amma yana ajiye wa Matansa abincin Shekara, don haka in sun ba shi ya gode, in ba su bashi ba, daman nasu ne.

Yana daga cikin kyautar Annabi (SAW), wata rana wani ya tava zuwa wurinsa yana neman taimako Annabi kuma (SAW) lokacin babu, sai ya nemo rancen rabin masaki na Dabino ya bashi. Wanda kuma ya bai wa Annabi (SAW) wannan rancen, da ya zo amsar bashinsa sai (SAW) ya ba shi Masaki cikakke. Annabi ya ce masa, rabin biyan bashi ne, dayan rabin kuma kyauta ce.

Allah
Dausayin Musulunci
+ postsBio
  • Dausayin Musulunci
    https://hausa.leadership.ng/author/dausayin-musulunci/
    Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi
  • Dausayin Musulunci
    https://hausa.leadership.ng/author/dausayin-musulunci/
    Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
  • Dausayin Musulunci
    https://hausa.leadership.ng/author/dausayin-musulunci/
    Kyawawan Halaye 2: Wasu Annabawa Da Sauran Bayin Allah Da Suka Yi Magana A Tsumman Jego
  • Dausayin Musulunci
    https://hausa.leadership.ng/author/dausayin-musulunci/
    Kyawawan Dabi’un Annabi Muhammadu (SAW)

MASU ALAKA

Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
Dausayin Musulunci

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
Next Post
Sharhi Kan Dabarun Noman Dabino A Nijeriya

Sharhi Kan Dabarun Noman Dabino A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Wasa 23 Da Eric Chelle Ya Gayyata Domin Buga Wasannin Sada Zumunci 

Duk Da Rashin Halartar ‘Super Eagles’ Gasar Kofin Duniya, Nijeriya Ba Ta Rasa Wakilai Ba

June 20, 2026
Sakamakon Ziyartar Kasar Sin Sau 13 Shugaban Myanmar Na Da Mahanga Dangane Da Salon Zamanantarwa Irin Ta Sin

Sakamakon Ziyartar Kasar Sin Sau 13 Shugaban Myanmar Na Da Mahanga Dangane Da Salon Zamanantarwa Irin Ta Sin

June 20, 2026
Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)

Hijira: Malaman Musulunci Sun Buƙaci  Musulmi Su Yi Riƙo Da Gaskiya Da Adalci

June 20, 2026
Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Rungumar Manufar Hadin Gwiwa Da Samun Ci Gaba Tare Da Kasar Sin A Fannin Kirkire-kirkire

Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Rungumar Manufar Hadin Gwiwa Da Samun Ci Gaba Tare Da Kasar Sin A Fannin Kirkire-kirkire

June 20, 2026
Nijeriya

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

June 20, 2026
Sin Na Kira Ga Al’ummun Kasa Da Kasa Da Su Himmatu Wajen Tallafawa Ayyukan Jin kai

Sin Na Kira Ga Al’ummun Kasa Da Kasa Da Su Himmatu Wajen Tallafawa Ayyukan Jin kai

June 20, 2026
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

Sojoji Sun Ceto Mutane 22 A Jihar Sakkwato

June 20, 2026
A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

June 20, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

June 20, 2026
IMF

Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

June 20, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.