A halin yanzu an kammala gasar wasan kwallon kafa ta duniya ta shekarar 2022 wadda hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) take shiryawa, kasar Katar ta dauki nauyin gabatarwa inda kasar Argentina, a kakrkashin jagorancin hazikin dan wasa Lionel Messi a karon farko cikin shekara 36 ta dauki kofin.
Masana harkar kwallon kafa a sassan duniya sun bayyana cewa, wannan gasar ita ce mafi tsari da aka taba yi a duniya.
- Kotu Ta Sake Hana DSS Cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- An Gurfanar Da Matashi A Kotu Sakamakon Lakadawa Dan Sanda Dukan Kawo Wuka
Haka kuma duk takaddamar da aka yi kafin a baiwa Katar damar daukar nauyin shirin an tabbatar da cewa, gasar na daya daga cikin gasar cin kofin duniyar da za a dade ana tunawa da ita a fadin duniya. Da farko an so a sanya harkar siyasa wajen kushe kasar amma yadda Katar ta sanya kwarewa da hikimomi wajen gabatar da gasar ya sanya ana ta yaba mata a fadin duniya a kan kokarin da ta yi.
Yana da muhimmanci a sani cewa, FIFA ta sanar da samun ribar fiye da Dala Biliyan 7.5 a tallace-tallacen da suka shafi shirin gasar a tsawon shekara 4 da aka sanar da gudanar da gasar a kasar Katar (Katar 2022). FIFA ta kuma bayyana cewa, ta samu karin fiye da Dala Biliyan 1 a kan kudaden da ta samu a tallace-tallacen da suka shafi gasar da aka gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018.
A karon farko a tarihin gasar kwallon ta duniya, kasar Afrika, Morroco ta samu nasarar kaiwa matakin kusa dana karshe inda ta zo ta 4 a gasar gaba daya. Sun samu nasara a kan kasar Belgium, kasace ta 2 a kwarewar kwallo a duniya wato Spaniya, ta kuma lallasa kasar Portugal a kan hanyar ta ta zuwa wasa na kusa dana karshe (semi-finals). Sun kuma yi namijin kokari a karawarsu da kasar Faransa wadda ke rike da kofin a gasar da aka yi a shekarar 2018, Morocco sun samu yabo daga masoya kwallon kafa a sassan duniya gaba daya.
Haka kuma kasar Senegal wadda ke rike da kambun gwarzuwar Afrika ta samu nasarar zuwa zagaye na biyu kafin kasar Ingila ta doke ta.
Yana da muhimmanci a fahimci cewa, dukkan tawagar Afrika da suka samu nasarar zuwa gasar ta Katar ‘yan asalin kasashen nasu ne ke horas dasu, wannan kuma wani babban darasi ne da ya kamata a dauka.
A farkon fara gasar ‘yan Nijeriya da dama basu ji dadin rashin kasancewa kasarsu a gasar ba. A ‘yan shekarun da suka gabata, ‘yan Nijeriya na ganin kasancewar kasar a gasar cin kofin duniya tamkar wani hakki ne nasu, za mu iya ganin dalilin haka ba tare da nisa ba.
Babu tantama Nijeriya na da kwarrarun ‘yan kwallo a ciki da wajen kasar amma mun kasa mayar da wannan baiwa zuwa cikakiyar nasara a filin wasanni, wannan kuma yana da nasaba da rashin iya gudanar da aiki na hukumomin kula da harkokin kwallon kafa.
A ra’ayinmu, a ‘yan shekarun da suka wuce harkar kwallo a Nijeriya tana kara tabarbarewa ne sannu a hankali. Tawagar ‘yan kwallon Nijeriya maza da mata basu samu nasarar shiga wasan Olampik da za a yi a kasar Tokyo ba, abin kuma da bai yi wa al’ummar Nijeriya masoya kwallon kafa dadi ba. A gasar cin kofin Afrika da aka yi an cire Nijeriya ne a zagaye na biyu, inda kasar Tunisia ta yi waje rod da su.
Da farko dai dole mu yi maganin dukkan matsalolin da bangaren hukumar kwallon kafa ke fuskanta. Dole a kawar da cin hanci da almundahana da ke tattare da hukumar kwallon kafan Nijeriya (NFF). Kwanakin baya ne babban mai horas da ‘yan wasan Nijeriya (Super Eagles), ya sanar da cewa, ba a bashi albashi ba na tsawon wata 6.
Albashin da dan kasar Portuguese ya kai dala 420,000 gaba daya, an dai dauke shi ne watan Mayun 2022 a kan albashin Dala 70,000 a duk wata.
Ministan wasanni, Sunday Dare, ya bayyana cewa, gwamnati za ta dauki nauyin biyan mai horaswar da zaran ya fara aiki amma hakan bai yiwu ba.
‘Yan Nijeriya da dama ba su yi mamakin wannan furucin ba, musamman ganin irin wannan furucin an dade ana yi a shekarun baya.
Idan za a iya tunawa a a halin yanzu ne hukumar NFF ke biyan bashin kudaden da tsohon kocin Super Eagles, Gernot Rohr yake bin hukumar bayan da aka dakatar da aikinsa a watan Disamban shekarar data gabata.
Haka kuma marigayi tsohon kocin Super Eagles, Stephen Keshi sai da aka kai ga yana bin bashin fiye da Naira Miliyan 35,000 a shekarun da yake horas da ‘yan kwallon Nijeriya.
A halin yanzu an dauki hukumar NFF matattara na biyan rabin albashi da cinhanci kuma ya zama dole a kawo karshen wannan lamarin.
A ra’ayin wannan jaridar,wadannan sune manyan matsalolin da suka zama tarnakin ga hana mu samun kwarrarun masu koyar da wasa, sai dai a tsaya ga matsakaitan masu koyar da wasa abin kuma da baya haifar da da mai ido, yakamata a kawo karshen wannan lamarin in har ana son a samu cikakken cigaba a harkar kwallon kafa a Nijeriya.
Mun kuma yi imanin cewa, mai horaswa dan kasa zai iya yin abin da ake bukata in har za a bashi dukkan abin da yake bukkata. Tun da aka dauko Peseiro a matsayin Kocin Super Eagles, al’amuran Super Eagles sai kara tabarbarewa suke cigaba da yi.
A ra’ayinmu, lokaci ya yi da za a sallame shi a kawo kwarren koci wanda zai fara shirya tawagar Nijeriya don zuwa wasan cin kofin duniya na shekarar 2026.
Muna bayar da shawarar a dauki wani sharraren tsohon wasan Nijeriya a kuma bashi damar tafiyar da harkokinsa yadda yake bukata a kuma bashi isashen lokacin yin aikinsa.
Kamar yadda muka bayyana a baya, Nijeriya nada kwararrun ‘yan wansan da za su iya kai kasar nan ga shiga gasar cin kofin duniya tare da daukar kofin, wannan shi ne burin dukkan ‘yan Nijeriya kuma yanazu ne lokacin fara tabbatar da wannan burin.