• English
  • Business News
Wednesday, July 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bankwana Da 2022: Daci Da Dadin Shekarar

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
in Labarai
0
Bankwana Da 2022: Daci Da Dadin Shekarar
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shekarar 2022, ana iya cewa shekara ce da Nijeriya ba za ta taba mantawa da ita a tarihance ba saboda abubuwan da suka faru na rashin dadi sakamakon matsalolin tsaro da kasar take fama da shi.

Yayin da kasar take bankwana da shekarar ta 2022, LEADERSHIP Hausa ta zakulo wasu manyan al’amura da suka faru a kasar.

  • An Fara Ginin Katafariyar Tashar Samar Da Lantarki Daga Hasken Rana Da Kafin Iska A Arewacin Kasar Sin
  • Kisan Lauya: Gwamnan Legas Ya Gana Da Sufeton ‘Yansanda

Janairu

Idan ba a manta ba, a ranar Talata 4 ga Janairun 2022, da misalin karfe 12:45 na rana, wasu ‘yan bindiga a kan babura su kimanin 300 zuwa 500 suka yi kawanya ga garin Kurfar Danya, inda suka kai kazamin farmaki. Wannan ya bude kofar kai sabbin hare-hare a yankun Kananan Hukumomin Anka da Bukkyum da ke Jihar Zamfara. ‘Yan bindigar sun yi tu’annati da yawa, bisa irin Harbin kai mai uwa da wabi da suka rika yi. Bugu da kari, sun shiga kauyukan Kurfa da Rafin-Gero inda suka shafe tsawon kwana biyu ba tare da an fatattake su ba. Kisan gillar da suka yi wa mutane a yankunan ya kawo karshe ne a yayin sojoji suka yi kukan kura suka afka wa ‘yan bindigar a ranar 6 ga Janairun 2022. An dai zargi Bello Turji da wannan aika-aikar.

Wani abu da Nijeriya ta fuskanta kuma shi ne, a ranar 14 ga Janairun 2022, wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Dankade da ke Jihar Kebbi, inda suka kashe daruruwan mazauna yankin, da banka wa shaguna da rumbunan hatsi wuta tare da sace garke-garken shanu. Bayan sun janye daga garin, an ga gawarwaki yashe a kan tituna.

Labarai Masu Nasaba

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Aminu Dantata

Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa

Fabrairu

A cikin watan Fabrairu ne al’ummar Jihar Bauchi ta shiga wani firgici bayan wani jirgi mai saukar ungulu da ba a gane kansa ba ya riga shawagi a yankin Lame-Burra da ke Karamar Hukumar Ningi ta jihar.

Har ila yau, a cikin watan, rashin tabbas game da bayanan ‘Yan Nijeriya a manhajar shaidar ‘yan kasa ta haddasa rudani saboda yadda aka hade rajistar layin waya da bayanan katin shaidar. Bugu da kari, a cikin Fabrairu ne layuka a gidajen man fetur suka fara bayyana, lamarin da aka ci gaba da fama da shi nan da can har zuwa karshen shekarar ta 2022.

Duk dai a watan na Fabrairu, an yi wa wasu ‘Yan Arewa kisan gilla a Jihar Abiya, mako daya bayan sake bude wata mayanka a garin Omumauzor da ke Karamar Hukumar Yamma a Jihar Abiya

Maris

A watan Maris kuwa, a ranar 8 ga watan, ‘yan bindiga sun kashe akalla dakarun ‘yan sa kai 62 a garin Sabaka da ke Jihar Kebbi. Haka nan duk dai a ranar, wani gungun ‘yan bindigar ya sake afka wa garuruwan Kanya da Wasagu/Danko. A nan ma sun yi barna bayan sun farmaki tawagar mataimakin gwamna tare da hallaka wasu jami’an tsaro da wasu mutum 8

Ranar 28 ga Maris ta 2022 kuwa, rana ce ta bakin ciki da alhini, domin a rannan ce aka kai wa jirgin kasan da ke zirga-zirga a tsakanin Kaduna da Abuja wani mummunan hari a kusa da Katari, harin da ya tilasta dakatar da sufurin jirgin na tsawon wata tara. An kai harin ne da misalin karfe 7:45 na almuru inda aka sace wasu fasinjoji da dama, wasu suka ji raunuka, wasu kuma suka riga mu gidan gaskiya.

Afrilu

A ranar 10 ga Afrilun 2022, gungun wasu ‘yan bindiga fiye da 150 sun rika kai hare-hare a Jihar Filato. An ruwaito cewa akalla mutum 70 ne aka sace aka yi garkuwa da su a yayin wannan harin.

A ranar 22 ga watan dai har ila yau, wani abin fashewa ya hallaka mutum 110 a wata haramtacciyar matatar mai da ke tsakanin iyakokin Jihohin Imo da Ribas.

Mayu

Har ila yau, a watan Mayu ne, ranar 12 aka kashe wata daliba da ke karatu a Kwaleji a Sakkwato, Deborah Samuel Yakubu, bayan an zarge ta da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) ta kafar sada zumunta ta WhatsApp.

Wakazalika, a dai watan na Mayu ne aka zargi Akanta Janar na Nijeriya, Ahmed Idris da wawure wasu biliyoyin nairori, lamarin da ya sa Shugaba Buhari ya dakatar da shi daga kujerarsa. An yi zargin ya yi sama da fadi da fiye da Naira Biliyan 80. Sai dai har yanzu ana shari’a a kai.

A ranar 28 ga watan Mayun 2022, mutum 31 sun rasa ransu, yayin da bakwai suka jikkata sakamakon turmutsitsi a garin Fatakwal da ke Jihar Ribas lokacin wani taro a coci sa’ilin rabon abinci.

Yuni

Haka kuma a ranar 5 ga watan Yunin 2022, an samu harin bam da harbe-harbe a cocin Katolika a garin Owo da ke Jihar Ondo. Akalla mutum 40 sun mutu, yayin da wasu rahotonni suka ce adadin ya kai 80. Wasu na zargin ‘yan kungiyar kishin Islama da ke yankin Afirka ta yamma ta kai wannan harin.

An dai gudanar da zaben gwamna a Jihar Ekiti a ranar 18 ga watan Yunin 2022, inda aka zabi sabon gwamna a Jihar Ekiti. A lokcin ne tsohon gwamnan APC, Kayode Fayemi wa’adinsa ya kai karshe kuma bai samu damar a kara zabensa ba karo na uku. Tsohon sakataren gwamnagtin jihar, Abiodun Oyebanji karkashin jam’iyyar APC ya samu nasarar hawa kan mulki bayan da ya doke abokin tarararsa na jam’iyyar SDP, Olusegun Oni da kuri’u kusan kashi 30 a zagayen farko.

Yuli

Sannan an gudanar da zaben gwamnan Jihar Osun a ranar 16 ga watan Yulin 2022, inda aka zabi sabon gwamna Jihar Osun. Tsohon gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APC, Gboyega Oyetola ya sha kaye daga dan takarar PDP, Ademola Adeleke da kuri’u kashi 3.5.

A ranar 7 ga watan Agusta, Tobi Amusun ‘yar shekara 16 ta kafa tarihi na samun nasarar lashe tseren mita 100 a gasar kasashen rainon Ingina ta shekarar 2022.

Agusta

A ranar 31 ga watan Agusta, mutum daya ya rasa ransa tare da jikkata shida sakamakon ruftawan gini a Jihar Kano.

Wani abu da za a ce ‘Yan Nijeriya sun sarara da shi kan matsalar tsaro, shi ne fara amfani da jiragen Tucano wajen murkushe ‘yan ta’adda da suka addabi kasa a cikin watan Agusta.

Har ila yau, a cikin watan ne, Gwamnatin Zamfara ta sanar da cewa kasurgumin dan bindiga Bello Turji ya tuba ya rungumi zaman lafiya. Lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce musamman a kan alhakin rayukan da aka kashe da sunansa.

Wakazalika, a watan ne aka zargi wasu sojoji biyu da halaka wani malamin Musulunci Sheikh Goni Aisami a Jihar Yobe.

Satumba

A ranar 5 ga watan Satumba, mutum shida suka mutu lokacin da gini ya ruguje a Jihar Legas. Sannan a ranar 12 ga watan Satumba, mutum biyar suka mutu lokacin da aka farmaki ayirin tawagar sanata a Anambra.

Duniya ta girgiza a ranar 8 ga Satumbar 2022, bayan an sanar da mutuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II wacce ta shafe shekara 70 a kan karagar mulki. Ta hau karaga daga watan Fabrairun 1952 zuwa 8 ga Satumbar 2022. Ta mutu tana da shekara 91 a duniya.

A ranar 17 ga Satumba, mutanen Kano da sauran sassan Nijeriya suka yi wayi gari da mummunan labari a kan kisan wata budurwa Ummulkulsum da aka fi sani da ummita wanda ake zargin wani dan kasar Sin da yi.

Ranar 21 ga Satumba, mutum 14 sun rasa ransu a garin Logo da ke Jihar Benuwe, inda ake zargin wasu makiyayan Fulani da kai wannan hari.

Ranar 24 ga Satumba, mutum 15 sun rasa ransu, yayin da mutane da dama suka raunata lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a masallaci a Jihar Zamfara.

Oktoba

A ranar 5 ga Oktoba, Rundunar sojojin Nijeriya sun bayyana cewa sun samu nasarar ceto fasinjoji har guda 23 wadanda aka yi garkuwa da su a watan Maris yayin da aka farmi jirgin kasan da ke jigila a tsakanin Abuja da Kaduna. Wannan ya alamta cewa an ceto dukkan fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin jirgin.

Haka kuma a ranar 8 ga Oktoba, mutum 76 sun rasa rayukansu lokacin da gwalegwale ya kife a Jihar Anambra.

Idan ana batun al’amuran da suka faru a Nijeriya a 2022, ‘Yan Nijeriya ba za su taba mantawa da batun tsawon yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta kawo karshe ba a ranar 14 ga Oktobar 2022, bayan ta shafe wata 8 tana yi.

Ranar 17 ga Oktoba, aka samu yawaitar mace-mace sakamakon ambaliyar ruwa a Nijeriya, wanda har sai da ya kai sama da mutum 600.

A ranar 18 ga Oktoba, an kashe mutane da dama, yayin da aka yi garkuwa da mutum 10 bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a asibitin Neja.

Nuwamba

Ranar 8 ga Nuwamba, mutum hudu sun rasa rayukansu tare da jikkata mutane 12 lokacin da bam ya tashi a Jihar Anambra.

Ranar 11 ga Nuwamba, mutum 12 sun mutu lokacin da tirelan mai ta fashe a garin Ofu da ke Jihar Kogi.

A ranar 23 ga Nuwamba ne Gwamnatin Buhari ta kafa tari, yayin da ta kaddamar da fara aikin hako mai a yankin Kolmani da ke tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe.

Disamba

A ranar 7 ga watan Disamba, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa zai rage yawan kudaden da mutum zai iya cirewa a ATM zuwa 100,000 a duk mako, domin rage yawan kudaden jabu da kuma magance biyan kudin fansa. Sai dai daga baya ya kara zuwa Naira 500,000 a mako.

Bugu da kari, a ranar 15 ga Disamba ne aka fara amfani da sabbi takardun kudin da CBN ya buga na Naira 200, da 500 da kuma 1000.

A ranar 18 ga Disamba, duniya ta shaida tarihin da kasar Argentina ta kafa tun bayan shekara 36, na lashe gasar cin kofin duniya da aka fafata a kasar Katar, bayan ta doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Sannan a ranar 20 ga Disamba, akalla mutum 38 suka rasa rayukansu, yayin da aka babbake gidaje bakwai lokacin wani hari guda biyu da ‘yan bindiga suka kai a kauyukan Kagoro a Jihar Kaduna.

A ranar 27 ga Disamba, mutane 14 suka mutu, sannan sama da 24 suka raunata bayan da wani bigaggen direba ya yi cikin taron dandazon jama’a a lokacin bikin gargajiya a Kalaba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 20222023BankwanaSabuwar Shekara
ShareTweetSendShare
Previous Post

Darussa Ga Nijeriya Daga Gasar Cin Kofin Duniya

Next Post

Sabon Matsayin Da Nijeriya Ta Koma A Jadawalin FIFA

Related

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Aminu Dantata
Labarai

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Aminu Dantata

33 minutes ago
Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa
Ra'ayi Riga

Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa

5 hours ago
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Labarai

Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza

8 hours ago
Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba
Manyan Labarai

Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba

9 hours ago
Dangote Ya Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 820
Manyan Labarai

Dangote Ya Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 820

11 hours ago
Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki
Manyan Labarai

Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki

12 hours ago
Next Post
Sabon Matsayin Da Nijeriya Ta Koma A Jadawalin FIFA

Sabon Matsayin Da Nijeriya Ta Koma A Jadawalin FIFA

LABARAI MASU NASABA

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Aminu Dantata

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Aminu Dantata

July 9, 2025
Akwai Bukatar Sin Da Masar Su Zurfafa Hadin Gwiwa Domin Kare Muradunsu

Akwai Bukatar Sin Da Masar Su Zurfafa Hadin Gwiwa Domin Kare Muradunsu

July 9, 2025
Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa

Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa

July 9, 2025
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe

Babu Wanda Ya BuÆ™aci Atiku Ka Da Ya Yi Takara A 2027 – ADC

July 9, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza

July 9, 2025
Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba

Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba

July 9, 2025
Dangote Ya Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 820

Dangote Ya Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 820

July 9, 2025
Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense

Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense

July 9, 2025
Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki

Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki

July 9, 2025
Sin Ta Ware Yuan Biliyan 10 Don Shirye-Shiryen Ba Da Tallafin Aiki

Sin Ta Ware Yuan Biliyan 10 Don Shirye-Shiryen Ba Da Tallafin Aiki

July 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.