Bayan makwanni ana zullumi a halin yanzu an kammala zaben game gari na kasar Kenya, inda William Ruto, mai shekara 55 a duniya, wanda kuma shi ne mataimakim shugaban kasar tun daga shekarar 2013 zuwa yanzu shi ne kuma shugaban jami’yya mai mulki ta ‘United Democratic Alliance’ ya samu nasarar lashe zaben kujerar shugaban kasar.
Ya samu nasara ne a kan Raila Odinga, mai shekara 77 a duniya wanda ya taba rike mukamin Firayministan kasar Kenya a tsakanin 2008–2013, shi ne kuma shugaban jamji’yyar ‘Orange Democratic Mobement’ a zaben da aka fafata matuka.
Sauran wadanda suka tsaya takarar a zaben sun hada da Dabid Waihiga Mwaure, shugaban jam’iyyar ‘Agano Party’ da George Wajackoyah, na jam’iyyar ‘Roots Party of Kenya’.
Hukumar zaben Kenya ‘Independent Electoral and Boundaries Commission’ (IEBC) ta sanar da cewa, Ruto ya lashe zaben ne da kashi 50.5 na kuri’un da aka kada da suka kai Miliyan bakwai da digo daya (7.1 million) yayin da wanda yake biye da shi, Odinga, ya tashi da kashi 48.9 wato kuri’u Miliyan shida da digo tara (6.9 million).
Wani abin takaici duk kuwa ba wai ba a yi tsammanin faruwar haka ba ne, shi ne yadda zaben ya bar baya da kura, musamman yadda kakaddamar da ta tasho a tsakanin hukumar zaben da kuma irin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben a wasu sassan kasar.
Hudu daga cikin bakwai na manyan jami’an zaben kasar sun yi watsi da sakamakon zaben, wannan yana zuwa ne duk da yawan hukumomin da suka sa ido a kan yadda aka gudanmar da zaben ciki kuwa har da jami’an Majalisar Dinkin Duniya wadanda rahoton su ya nuna cewa an yi zaben cikin kwanciyar hankali.
Abubuwan lura tare da daukar darasi a zaben kasar ta Kenya suna da yawa a zaben da ya gudana ranar 9 ga watan Agusta.
Zaben wanda ya kasance na samar da shugaban kasa na 5 tunda kasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1963, sun kuma zabi gwamnoni, ‘yan majalisar kasa da za su jagoranci majalisa ta 47 a tsarin majalisar kasar.
Shugaba Uhuru Kenyatta bai kasance a cikin masu takara ba kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ba zai shiga zaben Nijeriya na 2023 ba.
Yanayin yakin neman zaben bai kasance a kan abubuwan da suka shafi yi wa kasa aiki ba amma lamarin ya karkata ne tsakanin Odinga da Ruto inda suka mayar da hankali a matsayin kabila da asalin junansu, amma duk da haka an sanya muhawara a tsakanin ‘yan takarar.
Muhawarar ta samu cikas yayin da Odinga da kuma Wajackoyah suka janye daga shirin.
Odinga ya ce ba zai yi muhawara da Ruto ba, a bisa zargin cewa, ba shi da mutunci. Shi kuma Wajackoyah ya nemi a hada shi ne da ‘yan takarar shugabancin kasar su biyu a lokaci daya, bukatar da ta samu karbuwa a wajen masu shirya muhawarar.
Duk da haka rahotanni sun nuna cewa, an gudanar da zabubbukan cikin kwanciyar hankali a kasar duk cewa kuma an samu wuraren da aka dage zaben saboda matsalolin tsaro.
An kuma samu tsaikon kada kuri’a a wasu runfunar zaben saboda matsalar da aka fuskanta daga na’urar tantance masu kada kuri’a wanda ake kira ‘Kenya Integrated Elections Management Systems (KIEMS)’.
Hakan ta sanya hukumar IEBC ta bayar da izinin dakatar da amfani da na’urar a wasu runfunan zaben a yankunan Kakamega da Makueni yayin da ba a samu fara kada kuri’a a daidai karfe 6 na safen da aka ayyana ba saboda matsalar na’urar da aka samu.
Zuwa karfe 12 a ranar zaben, mutum 6,567,859 sun samu nasarar kada kuri’arsu wanda ke nuna kusan kashi 30 na wadanda suka yi rajistar kenan. Awa daya kuma kafin a rufe runfunan zaben na karfe 5 na yamma an samu mutum fiye da 12,065,803 da suka kada kuri’unsu, kashi 56.17 ke nan na wadanda suka yi rajistar zaben a kasar.
A ranar 10 ga watan Agusta 2022, hukumar zabe ta IEBC ta sanar da cewa, na’ura ta tabbatar da ‘yan Kenya Miliyan 14 suka kada kuri’arsu wanda hakan ke nuna kashi 64.6 kenan na wadanda suka yi rajistar zaben gaba daya.
Shugabar hukumar zaben IEBC, Wafula Chebukati, ta zargi wakilan jam’iyyu da yi wa tsarin tattara kuri’un zaben zagon kasa.
Kamar dai Nijeriya, Kenya na amfani da na’ura a matakai uku na zabe da suka hada da yin rajistar masu zabe da tantance masu kada kuri’a da kuma matakin aika da sakamakon zabe. Amma kuma ba kamar Nijeriya ba a Kenya ‘yan kasar da ke a kasashen waje na da ikon kada kuri’a a zabukkan da ake gudarnarwa suna kuma da ‘yan takara masu zaman kansu (Independent candidates).
Kwanaki uku bayan kammala zaben an samu nasarar tattara kashi 99.94 na sakamakin ta hanyar na’ura mai kwakwalwa sai dai kadan daga cikin wadanda basu shigo hannu ba suka rage da ba a tantance tare da sanar da su ba.
Duk da haka ne a ranar Litinin 15 ga watan Agusta hukumar zabe ta sanar da wanda ya lashe zaben.
Nan take Ruto ya amince da sakamakon tare da yin alakwarin jagorantar kowa da kowa a kasar a tare nuna banbanci ba, yayin da kuma Odinga ya yi watsi da sakamakoin zaben inda ya yi zargin an saba tanade-tanaden kundin tsarin mulki kuma sakamakon ya haramta, abin burgewa a nan shi ne ya nufi kotu ne don kalubalantar sakamakon zaben maimakon tayar da hankali al’umma.
A shekarar 2027 kasar ta fuskanci tarzomar zabe inda aka yi asarar rayukan mutum fiye da 1000 a wani rikicin kuma a shekatrar 2017 an yi asarar rayukar mutum 100, a kan haka mutane da dama ke fatan a samu nasara a zaben na wannan shekarar.
A mastayinmu na gidan jarida muna kira ga al’umma kasar Kenya su kai zuciya nesa, hakan na da muhimmanci ga dukkan masu ruwa da tsaki a kan su bi doka tare da ganin an gudanar da komai ba tare da an yi magudi ba.
Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin zaben Nijeriya su gudanar da abin da ya dara na kasar Kenya na tabbatar da an yi sahihin zabe a 2023.
Abin lura a nan kuma shi ne INEC na daga cikin hukumomin kasa da kasa da suka sa ido a yadda aka gudanar da zaben na Kenya. Tabbas an yaba mata a kan yadda ta gudanar da zaben jihohin Ekiti da na Osun to yakamata ta kara kaimi wajen inganta ayyyukanta a zaben 2023.
Muna kuma fatan ‘yan takarar shugabancin kasa za su yi koyi da takwarorinsu na Kenya ta hanyar tabbatar da su da magoya bayansu sun rungumi tafarkin zaman lafiya, kafin, yayin da lokacin da aka kammala zaben 2023.