ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Zamfarawa Suka Karbi Tuban Kasurgumin Dan Bindiga Bello Turji

Tubansa Ba Alheri Ba Ne – Barista Bulama

by Hussein Yero
4 years ago
turji

A farkon wannan makon ne Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji, ya tuba daga barnar da suke yi, ya rungumi zaman lafiya kuma har ma ya zamo mata kwamandan yakar wadanda suka ki amincewa da sulhu kamar yadda Mataimakin Gwamnan Zamfara, Sanata Hassan Nasiha ya bayyana.

Mataimakin gwamnan ya ce Bello Turji, ya rungumi shirin zaman lafiya, ya kuma daina kai hare-hare a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da kuma Zurmi da ke fadin jihar.

  • Wani Makusancin Gwwamna Wike, Prince Nwiyor, Ya Fice Daga PDP Ya Koma APC

Ya bayyana haka ne a wani taro kan harkokin tsaro a Gusau babban birnin Jihar Zamfara, wanda kungiyar dalibai ta Jami’ar Madina ta shirya, inda ya ce matakin da Turji ya dauka na samar da zaman lafiya a kananan hukumomin guda uku wadanda a baya suke kan gaba wajen hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya abin a yaba ne.

ADVERTISEMENT

A cewar mataimakin gwamnan na Jihar Zamfara, a cikin makonni biyar da suka gabata ba a samu wata arangama tsakanin Fulani da Hausawa a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi ba sakamakon tattaunawar sulhun da aka yi a tsakanin bangarorin biyu da ke fada da juna.

Ya bayyana cewa, Turji ya ba da umarnin a yi wa Gwamna Bello Muhammed albishir, domin a yanzu haka yana kaddamar da farmaki a kan ‘yan ta’addan da ake zargi a yankunan saboda tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo jihar.

LABARAI MASU NASABA

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

Sanata Nasiha ya kuma bayyana cewa kwamitin da Gwamna Bello Mohammed ya kafa a karkashinsa ya gudanar da taron zaman lafiya da sansanonin ‘yan bindiga guda 9 a gundumar Magami da Masarautar Dansadau ta kananan hukumomin Gusau da Maru ta jihar, domin dakatar da kai wa al’umma hare-haren da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ce Gwamna Matawalle ya bayar da umarnin a mayar da duk hanyoyin kiwo da filayen kiwo da ruwan da dabbobi suke amfani da sauran dukiyoyin Fulani da aka kwace a sakamakon rikicin da ya barke tsakanin su da Hausawa, kana ya ce a gaggauta mayar da su ga Fulani domin a samu zaman lafiya a kasa.

To ko yaya Zamfarawa suka karbi tuban Bello Turji ganin cewa akwai abubuwa marasa dadi da suka auku a tsakaninsa da al’ummomin gari?
Wani mazaunin garin Shinkafi, Malam Garba Gero ya nunar da cewa tuban Bello Turji abin lale marhabin ne domin wannan tsarin na sulhu shi ne zai taimaki yankinsu ya ceto su daga hadarin da suke ciki.

“’Yan’uwanmu na wajen Zamfara sun fid da rai daga gare mu tun da sun ba mu shawarwarin mutashi mun ki, kuma gashi sai kashe mu ake yi da sace mu, amma a yanzu Allah ya kawo karshen wahalar da muka sha a baya.
“Yanzu muna iya zuwa gonakinmu muna aiki ba tare da zullumi ba. Don haka muna murna da wannan sulhu na Turji da gwamnati ta amsa.”

Shi kuwa, Kabiru Moriki Direba, ya bayyana wa wakilinmu cewa, wannan sulhu alhairi ne.
“Domin yanzu haka mu direbobi ba mu tsoran hanya saboda ‘yan fashin daji, sai dai barayin gida masu amsar waya da kudi ba dai masu garkuwa da mutane ba. Yau wata biyu kenan mun samu kwaciyar hankali, fatar mu shi ne mu ga dorewarsa.”

Har ila yau, shi ma da yake bayyana ra’ayinsa, Hon. Abdullahi Muhammad Lakwaja Anka ya yaba wa Gwamna Matawalle bisa wannan namijin kokarin na maida ‘yan ta’adda mutanen kirki da ajiye makamansu tare da rungumar zaman lafiya.

“Muna kira ga Gwamna Matawalle da ya ci gaba a kan kokarinsa da yake yi na ganin su ma sauran ‘yan bindigan na yankin Anka, Gumi da Bukuyum sun aje makamansu. Tun da tsaurinsu ba su kai na Turji ba, amma gashi ta hannun Gwamna Matawalle an samu nasara a kan haka.
“Domin haka, muna yi wa kwamitin mataimakin gwamna a kan sulhu addu’a a kan samun nasara na dawamamen zaman lafiya a Jihar Zamfara gaba daya.”

Sai dai kuma, sauran ‘Yan Nijeriya masu lura da abubuwan da ke gudana na rashin tsaro a Zamfara, sun bayyana cewa bai kamata Bello Turji ya ci bulus kan abubuwan da ya aikata ba.
Mai sharhi kan ayyukan ‘yan ta’adda da harkokin yau da kullum, Barista Audu Bulama Bukarti ya ce sulhu da Turji ba zai haifar da da mai ido ba.

“Idan dai Turjin da muka sani ne wanda ya banka wa fasinjoji 23 ciki har da mace mai juna biyu wuta a Sakkwoto, yanzu kuma gwamnatin Zamfara ta ce ya tuba har yana taimaka mata wajen yakar ‘yan bindigan da suka ki yin sulhu, ba za mu yi mamaki ba idan gwamnatin ta saya masa makamai da motoci da sauran kayayyaki a matsayin yana taimaka mata.

“Har yanzu Turji bai yi nadama a kan kisan-kiyashin da ya yi ba. Domin a baya ya karya alkawarin da ya yi na sulhu. A yanzu haka yana zartar da hukunci a matsayin alkali na kisan wadansu ‘yan ta’adda, hakan ya ba shi lasisin ci gaba da kisan mutane kenan.

“Wannan sulhu zai iya kasancewa barazana, domin wasu gurbatattun ‘yan siyasa na iya amfani da shi a zabe mai zuwa wajen cimma burinsu. Lamarin zai kasance kamar alama ce ga sauran ‘yan ta’adda ta fuskar cewa abin da suke yi daidai ne kamar yadda Turji ya yi. Wannan ba zai haifar wa Jihar Zamfara da ma Nijeriya gaba daya da mai ido ba.” Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook da aka tabbatar nasa ne.

Bukarti ya kara da cewa ya kamata Gwamnatin Zamfara ta fito fili ta yi wa jama’a cikakken bayani a kan wannan sabon yunkurin nata amma ba ta fara gutsura labari ta bar shi ba kamar yadda ita ma Rundunar ‘Yansandan jihar ta yi gum da bakinta kan lamarin.
Shi dai Aye Bello Turji asalin sunansa shi ne Muhammadu Bello, an haife shi a garin Fakai da ke Gundumar Kware a karamar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara.

Shekarun Bello Turji ba su wuce 30 a duniya ba, ya taso ne a matsayin makiyayi karkashin mahaifinsa mai suna Kachalla.
Al’ummar yankin Fakai sun shaidi mahaifinsa a matsayin mutumin kirki, yana taka muhimmiyar rawa wajen sasanta kowacce irin fitina da ta taso a tsakanin Fulani da kuma Hausawa.

Mahaifin Turji ya bar yankin Shinkafi ne baki daya bayan da ya ga dansa Bello Turji ya dauki hanyar da ba ta dace ba, kuma ya yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya hana shi amma abin ya citura.
Bello Turji ya zama kasurgumin dan bindiga mai rike da makami tsawon shekara 7 da suka gabata. Ya bayyana daukar matakinsa ne da cewa sakamakon kisan da ‘yan kungiyar sa-kai suke yi wa Fulani tare da kona su da wuta, wanda a cewarsa ayyukansa na daukar fansa ne.

Bello Turji shi ne babban dan bindiga da ya addabi yankin Shinkafi a Jihar Zamfara da kananan hukumonin Isa da Sabon Birni da ke cikin Jihar Sakwato. Ya kashe mutanen da ko shi kansa bai san adadinsu ba a yankin karamar hukumar mulkin Shinkafi kawai. Akwai lokacin da a rana daya ya kashe sama da mutane 50 a yankin Kware, gundumar da ya fito.

A shekarar da ta gabata bayan da Gwamnatin Jihar Zamfara ta dauke layukan sadarwa na waya tare da kakaba dokar hana hawa babur da kuma takaita sayar da fetur a gidajen mai, ya mayar da hanyar Gusau zuwa Shinkafi kwata, inda a kullum sai an yi jana’izar mutane a Shinkafi wadanda yake kashewa a kan hanyar Kauran Namoda zuwa Shinkafi, haka kuma a kullum sai ya sace mutane matafiya ya kai su kauyensa na Fakai ana azabtar da su tare da neman kudin fansa.

Bello Turji ya farmaki garin Shinkafi safe da rana da kuma dare a lokuta mabanbanta har ma a masallaci ya kai hari ana tsaka da Sallar Magriba a garin Shinkafi, inda ya hallaka mutane 5 da raunata wasu da dama.
A watan Satumbar shekarar da ta gabata, ya rubuto doguwar takarda mai shafi uku zuwa ga Masarautar Shinkafi kargashin jagoranci Mai Martaba Muhammadu Makwashe Isa. Takardar na bayani ne a kan yana son a zauna lafiya kuma a ajiye makamai, sannan yana bukatar a isar da takardar zuwa ga Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawallen Maradun da kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Bello Turji ya tsagaita bude wuta da satar mutane tun bayan da ya aike wa mahukunta wannan takardar ta neman sulhu.

Mahukunta a karamar hukumar Shinkafi sukan tuntubi Bello Turji idan aka samu matsalar tsaro a yankin, kuma yana iya bakin kokarinsa wajen ganin an shawo kan matsalar.

A watanni hudu da suka gabata, wani dan bindiga ya bulla a yankin Shinkafi wanda dan asalin garin Maniya ne da ke gundumar Badarawa a karamar hukumar Shinkafi, mai suna Dullum. Dan bindigar yakan tare mutane a hanyar Kauran Namoda zuwa Shinkafi yana kisa da sace wasu kuma yakan shiga garuruwa yana kisan mutane, musamman a garin Badarawa, Jangeru, Baice, Birnin Yero da sauransu.

Bello Turji ya gargadi Dullum a kan ya ajiye makamai, amma ya ki amincewa da gargadin da Bello Turji ya yi masa, inda yaransa suka yi fito-na-fito da Turji, ya samu nasarar aika shi lahira.

Zuwa yanzu dai yankin Shinkafi ana samun saukin hare-haren ‘yan bindiga, sai dai ba a rasawa a wasu yankuna, kuma idan Turji ya kama Bafulatani da sunan kai hari yana zartar masa da hukuncin kisa ne nan take, in ji wata majiya.

Al’ummar Fakai da kewaye sun tabbatar da cewa suna rayuwa ne irin ta bayi, domin Turji shi ne gwamnati a yankin, duk abin da ya tsara shi ake bi, kuma wanda ya saba masa yana zartas masa da hukunci mai tsanani.
Daga cikin dokokin da ya sanya har da hade masallatai. A baya akwai masallatan Juma’a biyu (Tsohon masallaci da kuma sabo mallakin kungiyar Izala) wanda daga bisani Turji ya yi umurnin haduwa a masallaci na daya domin gabatar da Sallar Juma’a. Zuwa yanzu dai Turji bai yi umurnin kungiyar Izala ta ci gaba da gabatar da Sallar Juma’a a masallacinta ba.

A yanzu haka a yankin mazauna garuruwan ne ke yi masa kowane aiki, kama daga aikin noma da kuma aikin ginin gida da masallaci da yake gudanarwa yanzu haka a Fakai.

Turji
Hussein Yero
+ postsBio
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Ɗan Takarar Sanata A Zamfara Ya Koka Kan Yi Wa Rayuwarsa Barazana
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Abdulaziz Yari Ya Bukaci Limamai Su Ƙara Addu’a Kan Yaƙi Da Ƴan Bindiga A Zamfara
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Matawalle Ya Buƙaci Magoya Bayansa Su Mara Wa Shugaba Tinubu, Gwamna Lawal Baya
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Majalisar Zamfara Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi Biyu Kan Zargin Almundahanar Kuɗaɗe

MASU ALAKA

Turji
Rahotonni

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

May 17, 2026
Turji
Rahotonni

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

May 16, 2026
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada
Rahotonni

Almajiranci:Matsala Ko Maslaha

May 10, 2026
Next Post
goni

Kisan Gillar Sheikh Goni Aisami Gashuwa: Asalin Abin Da Ya Faru

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.