Kungiyar Shugabannin Arewa (NEF) ta zargi Shugaba Bola Tinubu da nadin mukaman gwamnati ba tare da daidaito tsakanin yankunan Nijeriya ba, wanda ta ce yana fifita yankin Kudu maso Yamma a kan sauran yankuna shida na kasar.
Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere, a cikin wata sanarwa a yau Juma’a a Abuja, ya bayyana cewa nadin da aka yi sun karkata ne wajen goyon bayan Kudu maso Yamma, yayin da sauran yankunan suka samu kadan ko kuma aka danne su.
- Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa
- Rurum Ya Shawarci Mafarautan Arewa Da Su Daina Zuwa Kudu FarautaÂ
NEF ta bayyana cewa wannan lamari ya sabawa tsarin hadin kan kasa, sannan ya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda a sashi na 2, da sashi na 14(3), ya tanadi cewa a kiyaye manufar adalci a nadin mukamai da rarraba albarkatun kasa.
Kungiyar ta kuma yi tir da sabon kwamitin kidayar jama’a na kasa, wanda ta ce yana da fifiko sosai a Kudu maso Yamma, wanda ke nuna rashin daukar wasu yankuna da muhimmanci. NEF ta yi kira da a sake duba wannan kwamitin domin tabbatar da daidaito tsakanin dukkanin yankunan kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp