Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan almajirai 17 da suka rasa rayukansu a sakamakon tashin gobara a makarantar islamiyya a karamar hukumar Kauran-Namoda da ke jihar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewar almajirai 17 ne suka rasu sakamakon gobarar da ta tashi cikin daren ranar Laraba.
- Gobara Ta Tashi A Wata Makarantar Allo Ta Hallaka Mutum 17, Ta Jikkata 16 A Zamfara
- Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamna Lawal ya Yaba Wa DSS Kan Bankaɗo Makamai A Jihar Zamfara
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanyawa hannu, gwamnan ya bayyana tsausayin kan faruwar al’amarin.
“Na kadu da samun labarin gobarar da ta kashe almajirai a makarantar Mallam Ghali a Kauran-Namoda”
“A madadin gwamnatin jihar Zamfara muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan daliban da suka rasa rayukansu da makarantar da gaba ɗaya yan Nijeriya bisa wannan ibtila’i”. A cewar Gwamnan
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da bai wa ‘yan’uwansu haƙurin jure wannan babban rashi, har ila yau gwamna Dauda Lawal ya yi addu’ar Allah ya bai wa wadanda suka samu raunuka lafiya.
Gwamnati za ta yi bincike domin ta gano dalilin afkuwar wannan gobara, domin kaucewa hakan a nan gaba.
A karshe ya ce gwamnati za ta bayar da duk wani taimakon da ake bukata da tallafi ga iyalan mamatan da kuma na asibiti.