Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce Daura zai koma da rayuwarsa da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa.
Bisa ga al’ada, Buhari ya kan zauna a babban gidansa na Kaduna kafin ya zama shugaban kasa, sai dai a yanzu ya ce garinsa na Daura ya fi masa.
- Farashin Kayan Masarufi Ya Kara Tashi A Abuja
- Buhari Ya Roki ASUU Kan Sake Duba Matsayarsu Ta Yajin Aiki
Sanarwar da fadar shugaban ta fitar a ranar Litinin, ta ce ya fadi haka ne a Daura inda yake gudanar da hutun Sallah.
“Nan da wata 10 zuwa 11, a nan zan dawo, ina da babban gida a Kaduna, amma ya yi kusa da Abuja,” in ji Buhari.
Buhari ya bayyana damuwa kan tasirin yajin aikin ASUU ga makomar ilimi da ci gaban Nijeriya, inda ya ce “yajin aikin ya isa haka nan.”
Ya ce duk da ya fahimci bukatunsu, amma za a ci gaba da tattaunawa yayin da dalibai ke ajin karatunsu.
Yajin aikin na ASUU abu ne wanda ke ci wa mutane da dama tuwo a kwarya, sai dai wasu na ganin gwamnatin ta Buhari na nuna halin ko in kula dangane da dorewar ilimi mai amfani a kasar nan.