- Ba Na Fatan Ko Makiyina Ya Shiga Hannun Masu Garkuwa
- Na Yi Ido Biyu Da Daya Cikin Wadanda Suka Fasa Gidan Yarin Kuje
BARRISTA HASAN LAWAL USMAN, na daya daga cikin mutane ukun da ‘yan ta’adda suka sako a ranar Litinin ta makon nan. Wakilinmu a Kaduna SHEHU YAHAYA ya garzaya gidansa da ke Unguwar Rimi a cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa inda ya tattauna da shi a kan irin darasin da ya dauka yayin zamansu a hannun masu garkuwa da mutane.
Daga cikin abin da ya bayyana a tattaunawar, akwai dalilin sakin faifan bidiyon da aka nuna ana ta dukan su a karshen mako wanda ya haifar da shakku a kan al’amarin tsaron al’ummar kasar baki daya. Ya ce duk da shakar iskar ‘yancinsa, har yanzu yana cikin damuwa saboda halin da sauran mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kadunan ke ciki a daji bayan kwashe watanni hudu.
Hakika wakilinmu ya tarar da shi cikin yanayi da jimami da tausayi tare da murna lamarin da ya sanya yana magana yana zubda hawaye bisa ganin yadda jama’a suka yi dafifi a kofar gidansu domin taya shi murnar dawowa gida.
Duk da yawan jama’a da suke gidan, Usman Hassan, ya dan ba mu lokaci a gurgije domin amsa wasu tambayoyi da muka yi masa inda a ciki ya bayyana cewa ba zai iya gane mazaunin da aka ajiye su ba, amma ba ya fatan ko makiyinsa ya kasance a irin halin da suka tsinci kansu a ciki.
Ka da mu cika ku da dogon bayani. Ga yadda hirar ta kasance:
Barrista Hasan Lawal Usman, ga shi ka fito daga hannun masu garkuwa da mutane, shin ya kake ji?
Alhamdu lillah! Magana ta gaskiya yanzu ga ni ina zaune cikin murna tare ‘yan’uwana da abokan arziki suna taya ni murna bisa irin halin da na samu kaina a ciki. Ina godiya ga Allah sosai.
Wanne irin yanayi suka ajiye ku yayin zaman ku a hannunsu?
Na farko dai, sun ajiye mu a wani kungurmin daji, inda a nan ne muke kwana a kasa daga nan sai muka samu wani abin shinfida muke shinfudawa a kasan bishiya muke kwanciya. Lokacin da aka fara ruwan sama suka yi mana wasu ‘yan rumfuna da zarar sun ga hadari ya taso, sai su kai mu ciki mu kwana. Amma gaskiya zaman wurin babu dadi ko daya domin ko makiyanka ka da ka yi masa fatan ya kasancewa a wurin.
Wasu sun ce sai da ‘yan’uwanku suka biya kudin fansa kana aka sako ku, ya abin yake?
Ammm! Gaskiya ba zan iya cewa an biya kudi ko ba a biya kudi ba kamin aka sako mu. Abin da na sani shi ne, ‘yan’uwa da abokan arziki sun yi yunkurin fitowa da mu, saboda gwamnati Nijeriya ta gaza a kan nauyin da ta daukar wa kanta na kare rayuwarmu da dukiyoyinmu.
‘Yan’uwanmu suka shiga cikin wannan halin suka je suna neman hanyar da za su fito da mu, amma mun samu labarin cewa gwamnati ta hana su su wuce domin su kubuto da mu, wanda jami’an tsaron suka hana su wucewa, sai dai duk da haka suka kara dawowa domin kubuto da mu, wanda yanzu ga shi sun samu nasarar kubutar da mu.
Toh! Ku nawa aka sako a wannan karon?
Eh! Mu uku ne, maza biyu sai mace guda daya.
Kamar ku nawa ne aka tsare a dajin?
Akalla mun kai arba’in (40).
Amma gaba daya ku nawa aka kama?
Mu sittin da hudu (64) ne.
Yanzu idan aka ce ka koma dajin, shin za ka iya gane dajin da aka ajiye ku?
Gaskiya ba zan iya ganewa ba.
Ko akwai wani yunkuri da kake ganin jami’an tsaro sun yi wajen kubutar da ku?
Gaskiya ba ni da wata masaniya a kan wani yunkurin da jami’an tsaro suka yi wajen kubutar da mu. Na san dai ranar Juma’a mu ukun da aka sako mun zo wurin da za a karbe mu, sai muka samu labarin cewa jami’an tsaro sun hana a fito da mu. Abin da na sani kenan.
Toh! Barista yaya batun abincin da kuke ci a dajin?
Gaskiya suna iya bakin kokarinsu wajen ba mu abinci daidai karfinsu. Wani lokacin har shanu suke yanka mana da awakai. Hatta ranar da aka sako mu sai da suka yanka mana sanuwa aka ba mu muka ci.
Ina gaskiyar labarin da muka samu na cewa wasu daga cikin ‘yan Boko Haram da suka fasa gidan yarin Kuje duk sun dawo dajin da kuke zama?
Eh! Gaskiya ne! Na yi ido biyu da daya daga cikinsu, saboda akalla akwai mutanensu kamar guda shida zuwa tara da suka dawo cikin dajin tare da ‘yan’uwansu, saboda a faifan bidiyon da aka aiko akwai guda daya da yake ikirarin cewa yana daga cikin wadanda suka kubuta daga gidan yarin Kuje.
Ina batun duka, an ce kullum suna lakada muku duka?
Gaskiya tun da muka je babu wanda ake duka har sai lokacin da wannan abun ya harzuka gwamnati, sannan suka fara dukanmu kamar yadda aka aiko a faifan bidiyon da aka turo. Gaskiya mun sha duka mutuka kuma sun ce wannan ma somin-tabi ne. Yanzu ma ina cikin jimamin halin da sauran ‘yan’uwa suke ciki, domin za su kasance cikin mummunar yanayi muddin dai ba a kawo musu dauki ba. Muna kira ga Gwamnatim Nijeriya da na kashen ketare da su taimaka su ceto sauran mutanan da suke tsare a cikin dajin.