Arsenal na dab da amincewa da yarjejeniyar daukar Declan Rice daga West Ham kan fam miliyan 100 kamar yadda rahotanni daga babban birnin kasar Ingila wato London suka bayyana.
Rice, mai shekara 24 kuma dan kwallon tawagar Ingila na iya koma wa Arsenal da tsada, idan aka hada da tsarabe-tsarabe kuma Arsenal din a shirye take ta dauki matashin a matakin mafi tsada da za ta saya a tarihin kungiyar.
- DSS Ta Gano Shirin Da Wasu Ke Yi Na Bata Sunan Gwamnatin Tinubu Kan Cafke Emefiele
- Abin Da Ya Sa Manoman Katsina Suka Mayar Da Martani Kan Alkwarin Gwamna Radda
Rice, dan kwallon tawagar Ingila wanda ya wakilci kungiyar a wasanni daban-daban ya fara kwallo daga karamar kungiyar West Ham daga baya ya koma babbar kungiyar ranar 1 ga watan Yulin shekara ta 2016.
West Ham United ta tabbatar cewar Rice zai bar kungiyar a karshen kakar nan kuma dan wasan ya lashe Europa Conference League a bana tare da West Ham, bayan da su ka ci Fiorentina 2-1.
Arsenal, wadda ta kare a mataki na biyu a teburin Premier League za ta buga Champions League a kaka mai zuwa kuma tana fatan lashe gasar firimiya a kakar wasa mai zuwa.