A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu.
Shugaban Amurka Trump ya ce, yana sa ran kasashen Sin da Amurka za su cimma matsaya kan batutuwan kasuwanci a taron kolin APEC da za a yi a mako mai zuwa, amma ya ce, watakila shugabannin Sin da Amurka ba za su gana ba a lokacin. Guo Jiakun ya yi wadannan bayanai ne a lokacin da yake amsa tambayoyi game da wannan batu, inda ya yi nuni da cewa, a halin yanzu babu wani cikakken bayani dangane da ganawar shugabannin Sin da Amurka.
Game da tattaunawar gaggawa tsakanin EU da kasar Sin kan batun hana fitar da ma’adanan farin karfe da kasar Sin ta yi kuwa, Guo Jiakun ya ce, yana fatan bangaren EU zai mutunta kudurinsa na nuna goyon baya ga cinikayya cikin ‘yanci, da adawa da kariyar cinikayya, da samar da yanayin kasuwanci na gaskiya da adalci da rashin nuna wariya ga daukacin kamfanonin kasashen duniya, da daukar kwararan matakai don kiyaye tattalin arzikin kasuwanci da ka’idojin hukumar kasuwanci ta duniya (WTO), da kafe kai da fata a kan amfani da tattaunawa da tuntuba wajen warware takaddamar kasuwanci yadda ya kamata. (Abdulrazaq Yahuza Jere)