‘Yan kasuwar man fetur sun bukaci a damke Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), Kanal Hameed Ali (ritaya), bisa sabawa hukuncin da wata babbar Kotun Tarayya (FHC) da ke Abeokuta, Jihar Ogun ta yanke kan kamawa da gwanjon motocin dakon man fetur 24 a matsayin tarkace.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Mai shari’a Shittu Abubakar na FHC Abeokuta, a ranar 9 ga watan Augusta, 2022, ya umurci hukumar da ta mayar da manyan motocin dakon man fetur guda 24 da aka kama ba bisa ka’ida ba daga ‘yan kasuwar man fetur zuwa ga masu su da kayan da ta dauko.
Amma, maimakon yin biyayya ga hukuncin da kotun ta yanke na mayar da manyan motocin ga masu su, sai Kwanturolan ya yi gwanjon manyan motocin da dukkan abubuwan da suka dauko.
Da yake magana a madadin ‘yan kasuwar man fetur a sakatariyarsu da ke Idiroko, Jihar Ogun, a ranar Talata, wakilin ‘yan kasuwar a bangaren shari’a na yankin Idiroko-Ipokia, George Oyeniyi, ya ce abin da ke cikin motocin 24 ya kai Naira biliyan 1.56.