Jiya Asabar 2 ga watan nan, wakili na musamman na shugaban kasar Sin, wanda kuma zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar ne, kana mataimakin firaministan kasar, Mista Ding Xuexiang, ya halarci taron koli kan sauyin yanayi tsakanin shugabannin kasashen G77 da kasar Sin a birnin Dubai, tare da gabatar da jawabi.
Jami’in ya ce, a matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, har kullum kasar Sin tana tare da sauran kasashe masu tasowa. Shugaban kasar, Xi Jinping ya jaddada cewa, “kungiyar G77 da kasar Sin”, muhimmin dandalin hadin-gwiwa ne tsakanin kasashe masu tasowa, kuma a ‘yan shekarun nan, Sin na himmatuwa wajen cimma burin kaiwa kololuwar fitar da iskar Carbon zuwa shekarar 2030, da kuma kawar da illar sa zuwa shekarar 2060. Kana, a yayin da take sauke hakkinta, tana kuma nuna hazaka wajen taimakawa kasashe masu tasowa, a fannin shawo kan matsalar sauyin yanayi.
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Kaddamar Da Dandalin Liangzhu
- CGTN: Kashi 90 Na Masu Kada Kuri’ar Jin Ra’ayi Sun Bukaci Burtaniya Da Ta Maido Da Kayayyakin Tarihi
Har wa yau, kasar Sin tana kokarin inganta hadin-gwiwar kasashe masu tasowa a fannin tinkarar sauyin yanayi, da shawarar “ziri daya da hanya daya” ba tare da gurbata muhalli ba, al’amarin da ya sa kasashe masu tasowa suka yi matukar maraba da shi.
Jami’in ya kara da cewa, akwai sauran-rina-a-kaba, dangane da kyautata ayyukan tinkarar sauyin yanayi a duniya. Kaza lika ya dace kasashen G77, gami da kasar Sin, su ci gaba da cimma matsaya daya, don kare hakkokinsu na bai daya. (Murtala Zhang)