A wani lamari mai ban mamaki na tsantsar gaskiya, wani direba mai shekaru 36, Safiyanu Mohammed, ya mikawa ‘yansandan jihar Kano wata jaka dauke da makudan kudade da ya tsinta.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdallahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
- Na Yi Alƙawarin Kawo Wa APC Kano A Zaɓen 2027 – Doguwa
- Gwamnati Ta Soke Kwangilar Aikin Titin Kano Zuwa Maiduguri
A cewar sanarwar, direban wanda mazaunin unguwar Rangaza kwatas ne a karamar hukumar Ungogo, ya tsinci jakar ne a ranar Juma’a 9 ga watan Agusta, 2024 a hanyar Hadejia kusa da mahadar Dakata.
A maimakon tafiya da kudin, Mohammed ya zabi ya mika wa hukumar ‘yansanda jakar da fatan za a gano asalin mamallakin jakar kudin.
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi kira ga jama’a da su taimaki rundunar da bayanan da za su kai ga gano mai kudaden.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp