Gwamnatin Tarayya ta rushe kwangilar gina Sashe na 1 na hanyar Kano-Maiduguri, wanda kamfanin Dantata and Sawoe Ltd ke aiwatarwa. Wannan kwangilar, wadda aka bayar tun a shekarar 2007, an soke ta ne saboda tsawon lokacin da ya ɗauka ba tare da kammala aikin ba.
Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ne ya sanar da hakan, inda ya kuma tabbatar da ɗaukar matakai nan take domin gyara sashen da ambaliya ta lalata a kan babbar hanyar Kano-Maiduguri a Jihar Bauchi.
- Saurayi Ya Raunata Budurwa Tare Da Barazanar Kisa Saboda Ta Ki Son Sa A Maiduguri
- Ambaliyar Ruwa Ta Katse Titin Kano Zuwa Maiduguri A Bauchi
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Barista Orji Uchenna Orji, ya fitar, Ministan ya umarci wata tawaga da su tantance ɓarnar da ambaliyar ta yi tare da kawo rahoto domin samar da mafita cikin gaggawa.
Ya jaddada buƙatar ƙara lura wajen aiwatar da ayyuka, yana mai nunawa cewa wasu ayyukan na lalacewa jim kadan bayan an kammala su, wanda hakan ke rage darajar su a dogon lokaci.
Ministan ya kuma haskaka ƙoƙarin da ake yi na inganta ɗorewa da ingancin ayyukan Gwamnatin tarayya, yana mai cewa za a iya sake duba lokacin da ake ba da garantin ayyukan.