Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin tabbatar da al’umma sun bi dokar hana zirga-zirgar adaidaita sahu daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan a wani sako da ya aike wa manema labarai da yammacin yau.
- Budurwa Ta Gudu Da Motar Saurayinta Bayan Ya Je Saya Mata Shawarma A Kano
- ‘Yan Sanda Sun Cafke Fursunan Da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje A Kaduna
Kiyawa ya ce, an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar Kano.
Ya kara da cewa an tanadi jami’an tsaro domin tabbatar da wannan doka kuma duk wanda ya karya dokar, tabbas doka za ta yi aiki a kansa.
Da safiyar wannan rana ne dai gwamantin jihar Kano, ta fitar da sanarwar hana zirga-zirgar adaidaita sahu a fadin jihar daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe, kuma dokar zata fara aiki ne a ranar Alhamis, 21 ga wannan watan.