A jajibirin ficewarsa daga ofis a watan Mayun 2023, Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari; ya amince da kudirin dokar kafa Hukumar Fansho ta Kasa da kuma al’amuran da suka shafi ‘Yan Majalisar Tarayya da Majalisar Dokoki (NASS), ta gabatar a gaban Majalisar Dokokin; domin nuna son kai da kuma isa ta Majalisar, yayin da kawai manufar wannan doka it ace; cire ma’aikatan majalisar dokoki (NASS) daga tsarin bayar da gudunmuwar Fansho (CPS), tare da mayar da su zuwa tsarin Fanshon da aka fi sani da ‘Defined Benefit Scheme’ (DBS) a turance, don kawai a kashe kudin jama’a tare da lalata dukiyar kasa.
Hukumar Majalisar Dokokin (NASS), ta dauki wannan mataki ne; bayan kebewar da aka yi na bai wa Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (HCSoF) da Manyan Sakatarori (Perm. Secs), bisa ga ra’ayin sha-ka-tafi wanda tsohon ministan shari’a ya bayar.
An yi komai na dokar fanshon majalisar dokokin ne a lullube, cikin sirri da rufa-rufa; an kuma yi gaggawar zartar da shi saboda zalunci. Wannan matakin dai ya yi daidai da yi wa ‘yan Nijeriya da Nijeriyar kwanton bauna da rana tsaka.
Har yanzu dai, sashen fansho na cike da rudani dangane da irin wannan yunkuri na ‘yan majalisa da ya kara dagula tsarin fanshon CPS, ta yadda hakan ya jefa shirin cikin hadari tare da haifar da rashin jituwa a tsakanin ‘yan kasa, wanda hakan ya kara raba hadin kan da kasar ke fatan samu.
Shagalin Majalisar Dokoki
Kudirin Hukumar Fansho ta majalisar dokoki (NASS), ya gabatar da tsarin fansho na musamman, wanda ke bai wa ma’aikatan majalisar dokokin fansho; wanda ba a taba ganin irin sa a duniya ba. A halin yanzu dai, akwai wadanda suka yi ritaya babu adadi; amma har yanzu ba su samu garatuti ko fanshonsu ba, ko kuma duka biyun; sannan bashin fanshon na karuwa a kan gwamnatin tarayya da kuma jihohi.
Wannan fansho na shagali ya hada da:
Kebe su daga tsarin CPS, wadda ita ce ginshikin biyan fansho na ma’aikatan gwamnati a Nijeriya. Wato za su ci albashinsu kashi 100, su kuma ci fanshon nasu kashi 500.
Kara shekarun yin ritaya daga shekaru 60 zuwa 65.
Cancantar wannan shagali shi ne, yin hidima ga majalisar dokoki na tsawon shekaru 40 ko kuma idan ma’aikaci ya kai shekaru 65 a raye.
Yin ritaya na kashin kai, ya cancanci a ba shi wannan shagali bayan akalla shekaru 10 yana yi wa majalisa hidima.
Fanshon Ma’aikatan Majalisan Dokoki, doka ce a cire kudaden daga lalitan gwamnatin taraya na CRF.
Kudirin ya bai wa dan fansho damar yin ritaya mai karamci gami da ba da fanshon da ya kai kashi 100 na albashinsa na shekara-shekara, wato kashi 500 cikin 100. Wadannan dimbin kudade da za a dinga biya, bayan an yi ritaya ya fi abin da yawancin ma’aikata ke karba; sannan kuma za a biya su ne a lokacin fara hutun watanni uku na wajibi. Ko shakka babu, wannan abin mamaki ne kwarai da gaske!
Ba da garatuti mai yawa da ya kai kashi 300 cikin 100, bisa albashinsu na shekara-shekara.
Izinin ganin likita da kula da lafiyarsu, har zuwa abin da ya kai kashi hamsin na albashinsu na shekara-shekara; wato kashi 50 cikin 100.
Kwatanta wannan zalunci da ake yi wa dukiyarmu da dukiyar kasa da yadda akasarin gwamnatocin jihohi da kuma gwamnatin tarayya suka ki kara mafi karancin albashi daga Naira 30,000 har zuwa yau!
Su Ne Wuka Kuma Nama Na Hannunsu
Bisa wannan doka, tsarin fansho a yanzu na fuskantar babban kalubale na tauye shi daga kowane bangare na ma’aikatan Nijeriya a cikin wannan numfashin, sannan kuma sabuwar dokar ta take tare da wulakanta wasu dokoki, manufofi, tsarin ayyuka da dai sauransu.
Dokar fansho ta malisar dokoki, ta ci karo da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na ci gaba da rike ma’aikatan gwamnatin tarayya karkashin tsarin CPS, kamar yadda yake kunshe a cikin farar takarda ta shekarar 2012 (White Paper); kan rahoton kwamitin shugaban kasa, kan sake fasalin gwamnatin tarayya da kuma tabbatar da aniyar gwamnatin tarayya a kan wannan tsari.
Majalisar dokoki ta kasa, ita ce mafi girman hukumar da aka kafa; don daidaitawa, hadewa da kuma daidaita ma’aikatan gwamnati a kan batutuwan da suka shafi ma’aikata, tsarin albashi, tantance ma’aikata da kuma sharuddan tsare-tsare na ayyuka. Amma an yi watsi da wannan doka a nan.
HCSoF, ita ce ofishin da ke ba da shawara kan shekarun ritayar ma’aikatan gwamnatin tarayya ta hanyar dokokin ma’aikata. A bisa wannan doka a yanzu, an cire ma’aikatan majalisar daga cikinta.
Bugu da kari, kudurin dokar bai yi la’akari da shari’a da da’a ba, domin ba a bi tsarin da ya dace na dokar ba tare da rashin jin ra’ayoyin jama’a da kuma rashin samun bayanai daga masu ruwa da tsaki.
Gidan Gata
Dokar fansho ta malisar dokoki, ta kara nisanta tare da raba kan al’ummar Nijeriya baki-daya tare da yin tasiri a kan tsarin gudanar da mulkin son kai da muke gani a Nijeriya a yau.
Majalisar dokoki, (wanda ake kira zababbun wakilai da ma’aikata), don kawai samun kansu a cikin zauren majalisar dokokin, sun bayyana kansu a matsayin manyan mutane sama da dukkanin wata doka, sannan kuma suna aiki ne don kansu tre da fifita bukatun mambobinsu a kan abubuwan da suka shafi kasa da kuma walwalar ‘yan kasar.
A gabanin wannan doka ta fansho mara tsarki, wadda malisar dokoki ta kafa akwai:
- Asibitin kanta
- Kasafin kudinta
- Ma’aunin albashinta
- Tallafin mazabarta, (Constituency allowance)
- Nan ba da jimawa ba, za ta kafa babban bankinta da kuma kasuwarta!
Wasa Da Hankalin ‘Yan Nijeriya
Dalilan da ba su da ma’ana, wadanda suka saba bayarwa su ne:
Suna da Muhimmin Matsayi: Cewa aikinsu na da muhimmanci ga shugabanci, dokoki, da kuma sa ido. (Ma’ana, Nijeriya za ta daina wanzuwa ba tare da malisar dokoki ba!)
Suna cikin Hatsari Da Damuwa: Cewa matsayinsu ya kunshi damuwa, hadari, daukar dogon lokaci, binciken jama’a da matsin lamba na siyasa, don haka sun cancanci fakitin ritaya mai karamci. (Sun manta su bayin ’yan Nijeriya ne kawai!)
Jan hankali Da Hazaka: Ta hanyar ba da fa’idodi na musamman, suna nufin rike kwararrun ma áikata. (Amma a cikin duniyar rayuwa, ba su da kwarewa irin ta rayuwar)
Tarihi: Suna nuni ne ga abubuwan da majalisun da suka gabata suka kafa. (Yin abin da bai dace ba yanzu, ya zama sabuwar al’ada da abin yabawa a Nijeriya!)
Sakamakon
Idan aka bar wannan ya tsaya, batutuwan da suka dace; kamar biyan kudin fansho, habaka gibin kasafin kudi, yiwuwar nauyin basussukan da ke tattare a kan asusun hadin gwiwar shiga ta tararya, gyara shekarun ritaya da dai sauransu, na nufin za su dawwama a kan kujerunsu har abada.
A halin da ake ciki, al’ummar Nijeriya na karuwa; sannan kuma babu wani abu da suka shuka wanda zai kula da wannan zamani da na gaba, ciki har da jikoki da tattaba kunensu.
Tashin Hankalin
Kungiyoyin Ma’aikatan Asusun Fansho (PFAs), Masu Kula da Asusun Fansho (PFCs), Jami’an Asusun Fansho na Rufe (CPFAs), Hukumar Fansho ta Kasa (PenCom), da Kungiyar Ma’aikatan Asusun Fansho ta Nijeriya (PenOp), duk sun yi Allah-wadai da wannan la’ananniyar doka.
Tambaya a nan ita ce, shin Nijeriya za ta iya tsira daga wannan zubar jini da take yi kuwa?