Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Fagge, Hon.Barista Muhammad Bello Shehu ya bayyana cewa su kan su a cikin ‘yan majalisun tarayya akwai ‘yan kudu da ba sa goyon bayan wannan doka ta harajin BAT.
Ya yi nuni da cewa ba a ce kar azo ayi wannan doka ba, amma maganar da suke shi ne na farko mene ne na yin sauri a dokar, ita dai doka musamman irin wannan da za ta taba rayuwar mutane abita daki-daki kafin a kai ga kaddamar da ita ace ta zama doka.
- Ali Nuhu Ya Zama Jakadan Kamfanin Tsaftace Haƙora A Arewacin Nijeriya
- Yaki Da Fatara: Gudummawar Sin Da Tasirinta Tsakanin Kasashen Duniya
Hon. Brr. MB. Shehu ya kafa misali da cewa a halin da ake ciki game da dokar mafi yawansu yan majalisu ma ba su fahimci ma me dokar nan take kunshe da shi ba, dan majalisa da bai fahimta ba, ta yaya zai koma gida ya fahimtar da mutanen sa suma su fahimta.
Ya ce abu ne da yake bukatar lokaci a fahimci dokar sanan su koma gida su fahimtar da mutane ga halin da ake ciki. Amma dai dokar nan ba su ga inda za ta iya zamewa Nijeriya bama Arewacin kasar nan alkhairi ba.
Hon. Barista Muhammad Bello Shehu ya ce misali akwai sashi a dokar da yake maganar” harmonising tad” wanda ya shafi tattara kudade da ake bai wa” TETfund “da harkar fasaha da na sadarwa duk a kudaden harajin ake dan gutsurar wani abu ake basu, yanzu in aka ce an tattare harajin nan sun koma wani asusun na daban guda daya ana tunanin jami’o’i na Najeriya ba za su iya ci gaba da gudanar da gine-gine da samar da abubuwa na zamani na bunkasa ilimi da sauran abubuwa makamantan wannan na ci gaba ba.