Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci jihohin Arewa 19 da su tsaya da ƙafarsu su jajirce su yi magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki.
Gwamnan ya jagoranci taron ranar farko ta bangaren Zuba Jari da Bunƙasa Masana’antu ta Arewacin Nijeriya a ranar Litinin a otel ɗin Abuja Continental.
- Ƙungiyar ASUU Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 14 Ta Biya Buƙatunta
- FCT Ta Amince Da Naira Miliyan 8.2 Kan Kujerar Aikin Hajjin 2026
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Ƙungiyar Dattawan Arewa ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ce ta shirya taron zuba jarin.
Sanarwar ta ƙara da cewa, taken taron shi ne “Buɗe Dabarun Damarmaki”, kuma ya tattaro duk masu ruwa da tsaki a sassan Arewacin Nijeriya.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya yaba wa Ƙungiyar Dattawan Arewa bisa jajircewar da take yi wajen ci gaban yankin Arewa.
“Ta hanyar kiran wannan taro a ƙarƙashin taken ‘Buɗe Dabarun Damarmaki,’ kun sake nuna kyakkyawar manufar ku kan makomarmu baki ɗaya.
“Bangarori kamar – Ma’adinai, Noma, da Makamashi — ba bisa haɗari aka same su ba, ginshiƙai ne waɗanda dole ne a gina su don ci gaban Arewacin Nijeriya. A Zamfara muna sane da halin da muke ciki: ƙasa mai albarkar ma’adanai masu tarin yawa da ƙasar noma, amma duk da haka mutanenmu ba su ci cikakken ribar waɗannan abubuwan ba.
“Muhimmin tambaya a gare mu a matsayinmu na shugabanni ba shi ne yin abin da ya kamata ba, amma ta yaya za mu iya juya akalar abin da ake muke da shi zuwa ci gaban al’umma. Don jawo jarin da ake buƙata da kuma samar da masana’antu a yankinmu don amfanin al’umma, dole ne mu tsaya haiƙan, mu rungumi sabuwar hanyar haɗin gwiwa.”
Gwamna Lawal ya ci gaba da jaddada cewa, Arewa mai zaman lafiya, Arewa ce mai ƙarfin tattalin arziki, yanki ne da ya kamata shugabannin jihohinta 19 su zurfafa haɗin gwiwa fiye da siyasa.
“Dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kare mutane da saka hannun jari. Tsaro shi ne babban abin da ake buƙata na duk wani ci gaba mai ma’ana. Masu zuba jari, na cikin gida da na lasa da ƙasa, ba masu hannu da shuni ba ne; su masu gaskiya ne. Ba za su saka jari a inda babu tsaro ba. Dole ne mu haɗa ƙarfin tsaron mu, mu raba hankali a cikin haƙiƙanin lokaci, da kuma samar da manyan jami’an tsaro na al’umma don samar da ingantaccen tsaro.
“A Zamfara, ƙoƙarinmu a fili yake, mun ƙaura daga halin da ake ciki a da na rashin gaskiya da rashin bin doka da oda a fannin ma’adinai zuwa yanayin na gaskiya da amana. Mun farfaɗo da harkar noma ta hanyar inganta noman zamani, sarrafa kayan noma, da samun rance. Kuma muna samar da yanayi mai tsaro da kwanciyar hankali wanda shi ne ƙashin bayan komai.
“Kirana a yau shi ne Yarjejeniyar Tattalin Arziki na Arewacin Nijeriya — alaƙar mai ƙarfi tsakanin jihohi 19 da su yi magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki. Samar da hanya guda ɗaya ga manyan masu zuba jari da ke neman yin kasuwanci a faɗin yankin. A hafa hannu a muhimman ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da jirgin ƙasa, igiya mai ƙarfi da zara haɗe jihohin mu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp