Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta ‘Amnesty International’, ta ce, ya zamana waja ga gwamnatin tarayyar Nijeriya ta daina barazana da tsorata mutane da kungiyoyi don sun soki ta a kasar.
A sanarwar da kungiyar ta fitar a shafinta na Tiwita, ta ce dole ne gwamnatin tarayya ta daina janyo tashin hankali da barazana ga mutane ko kungiyoyi kawai don sun bayyana ra’ayin fadin albarkacin bakinsu, domin a cewar kungiyar irin wannan barazanar ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da ma dokokin kasa da kasa.
- Bututun Iskar Gas Ya Sake Fashewa A Ribas
- Gwamnatin Kano Ga Ma’aikata: Duk Mai Bukatar Aikinsa Dole Ya Gabatar Da Kansa A Wajen Tantancewa
Kungiyar ta yi tur da zargin barazana da cin mutuncin da wata ‘yar yi wa kasa hidima da ke Legas, Ushie Uguamaye ta fuskanta.
Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyon da ta sake a manhajar Tiktok, inda take sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu dangane da wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon sauye-sauye kan tattalin arziki.
Kungiyar ta yi Allah wadai da barazanar da ake yi wa Uguamaye, tana mai cewa mutane na da ‘yancin bayyana ra’ayinsu kan wahalar da suke sha a bangaren tattalin arziki.
Kungiyar ta ce a maimakon neman cin mutuncin Uguamaye kamata ya yi gwamnatin tarayya ta dukufa neman kawo sauyin da zai rage wa jama’a wahalhalun da suke fuskanta da magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp