A wani gagarumin yunƙuri na shawo kan matsalar tsaro da kuma munanan laifukan da ke faruwa a yankin masarautar Yauri, Shugaban ƙaramar hukumar Yauri, Abubakar Shuaibu Ƙauran Yauri ya kira taron gaggawa da shugabannin ƙungiyoyin ‘yan banga. Babban maƙasudin taron dai shi ne warware matsalar jagororin da ta daɗe tana kawo cikas ga ƙoƙarin yaƙi da barazanar tsaro a ƙaramar hukumar.
A yayin taron, ƙauran Yauri, ya jaddada muhimmancin haɗin kai a tsakanin ƙungiyoyin ‘yan banga, inda ya jaddada cewa, dole ne a aje yin ɓangaranci domin samun ci gaba ta fuskar samar da tsaro a ƙaramar hukumar ta Yauri.
- Gwamnatin Kebbi Ta Kafa Kwamitin Kwato Kuɗaɗen Da Aka Sace A Asusun Marayun Jihar
- Sojojin Sama Sun Lalata Makaman ‘Yan Ta’adda, Sun Kashe Masu Yawa A Kebbi Da Zamfara
Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar ta sayo kayan aiki don rabawa ga dukkanin ƙungiyoyin ‘yan banga a faɗin ƙananan hukumomin 21, amma zaman lafiya a tsakanin ƙungiyoyin na da matuƙar muhimmanci wajen amfani da waɗannan kayan don in babu haɗin kai gwamnati ba zata yi aiki da ɓangaranci ba.
Shugaban ya yabawa ƙoƙarin Gwamna Nasir Idris na tallafawa ƙungiyoyin ’yan banga, musamman ma ƙudirin sayo sabbin motocin sintiri ga ɗaukacin ƙananan hukumomi 21.