Shugaban Ƙungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, Dakta Abubakar Ɗantsoho, ya bayyana cewa, dole ne Afirka ta mayar da hankali wajen amfana da damarmakin da ke Tekunanta, domin ƙara bunƙasa tattalin arzikinta.
Ɗantsoho, wanda kuma shi ne, Shugaban Hukumar Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa NPA, ya sanar da hakan ne,a jawabinsa a taron Daraktoci da ƙwararrun masu kula da kafar sanada zumunta ta zamani na ƙungiyar ta PMAWCA da ya gudana a yankin Luanda, na ƙasar Angola.
- Mamakon Ruwan Sama A Wasu Jihohi Na Barazana Ga Harkokin Yau Da Kullum
- Remi Tinubu Ta Bada Gudunmawar Naira Biliyan 1 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwan Neja Ta Shafa
Shugaban ya ce, Afirka ita ce, kan gaba wajen kula da Tekunan Ruwa, inda ya ƙara da cewa, sauran ƙasashen da ke Afirka ta Gabas da kuma waɗanda ke a Afirka ta Tsakiya, ba wai kawai suna kula ta Tekunnansu bane, har da ma musharaka da sauran irin ƙalubalen da suke fuskanta da sauran damarmakin da suke amfana da su.
“Yanzu ne, lokacin da ya dace, ake da matuƙar buƙatar mu amfana da sauran damarmakin da ake da sun a Tekuna, “ Inji Ɗantsoho.
“ Dole bai kamata ace, mun fitar da rai ba, wajen una irin ƙarfin iya shugabancin da muke da shi, na shugabantar Tashoshin Jiragen Ruwa, musaman domin ɗorewar muradun ƙarni wato SDGs, domin ci gaba da ɗorewar duniya, musamman Afrika, ta hanyar ci gaba da bai wa Tashohin Ruwan kulawarda ta dace, “ Acewar Shugaban.
“Baya ga alaƙa da Ruwa, ƙasashen da ke Afirka ta Gabas da kuma waɗanda ke a Afrika ta Tsakiya, da suke yi musharaka da irin ƙalubalensu da kuma sauran damarmakinsu, dole ne mu zage mu amfana da tattalin arzikin da ake da shin a Tekuna, musamman ta hanyar haɗa kanmu da kuma yin haɗaka, wanda idan ba a yi hakan ba, tamkar muna kawai yaudarar kawunan mu ne,” Ɗantso ya ce.
A cewar Shugaban na Hukumar NPA, alƙaluman da ake da su, sune za su bamu damar, ci gaba da ɗaukar matakan da suka kamata, na wajen ci gaba da bai wa Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika, kulawar da ta dace.
Kazalika, Shugaban ya kuma jinkinawa shugaban ƙasa Bola Tinubu, kan ƙirƙiro da Ma’aikatar Kula da Tattalin Arziki na Teku, inda ya sanar da cewa, hakan ya samar wa da Hukumar ta NPA sauƙi wajen samar da inagantattun sauye-sauyen a fannin na tafiyar da Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar.
“Gwamnatin mai girma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙirƙiro da Ma’aikatar Kula da Tattalin Arziki na Teku, hakan ya samar wa da Hukumar mu ta NPA samun sauƙin samar da ingantattun sauye-sauye, a fannin na tafiyar da Tashoshin Jiragen Ruwan Ƙasar nan, inda kuma ta hanyar Ma’aikatar, a ƙara samar da ɗimbin masu zuba hannun jari a fannin tare da kuma amfana da basira ƙwararrun da ke a ƙungiyar ta PMAWCA,” Inji Shugaban.
Ɗantsoho ya ci gaba da cewa, ƙwararrun da ke kula da kafar sadarwar, suma suna ci gaba da taimaka wa wajen ƙara samar da horo domin a amfana da damarmakin da ke a Tashoshin na Jiragen Ruwan, musamman ta hanyar amfani da tsarukan PCS NSW.
Shugaban na Hukumar ta NPA ya ƙara da cewa, dole ne, a ci gaba da yin ƙoƙarin da ake gudanarwa kafaɗa da kafaɗa, ta hanyar haɗa kai da sauran ‘ya’yan ƙungiyar ta PMAWCA.
“Manufofin yarjejeniyar kasuwanci marar shinge ta Afrika wato AfCFTA, sun haɗa da kawar da haraji da kuma duk wani harajin da ke sanya wa, na gudanar da hada-hadar kasuwanci, wanda hakan zai kuma ƙara samar da sauran damarmaki a fannnin da kuma ƙara samun ɗaukaka fannin,” Inji Ɗantsoho.
Ɗantsoho ya ƙara da cewa, a taron da Dakaratocin na ƙungiyar ta PMAWCA suka gudanar, sun yi nazari kan samakon ayyukan da ƙungiyar ta gudanar shekarar 2024 tare da kuma auna shawarwarin da mahalarta taron suka bayar, a lokcin taron, inda suke tsara matakan da za su ɗauka nag aba, domin ƙungiyar, ta ƙara samun ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp