A yau Talata ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta jagorancin taron manema labarai da aka saba yi, inda ta amsa tambayoyi game da matakin kawo cikas ga tsarin samar da hajoji da Amurka ta dauka, bisa hujja wai “Ana tilasta yin aikin kwadago”.
Ta ce, sau da dama, Sin ta ba da shaidu dake nuna cewa, zargin tilastawa mutane yin aiki a yankin Xinjiang ba gaskiya ba ne, don haka dole ne Amurka ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin bisa wannan hujja, kana ta kauracewa shafawa kasar Sin bakin fenti.
- Wang Yi: Kasar Sin Za Ta Ba Da Sabbin Gudummawa Don Bunkasa Harkokin Kare Hakkin Dan Adam Na Duniya
- Manyan Jami’an JKS Sun Mika Rahoton Ayyukansu Ga Kwamitin Kolin Jam’iyyar
Yayin da aka tabo batun taron kwamitin kare hakkin Bil Adama karo na 55 na MDD da ake gudanarwa kuwa, Mao Ning ta ce, Sin za ta ingiza shawarwari, da hadin kai tsakanin bangarori masu nasaba, kan batun hakkin Bil Adama, ta yadda za ta taka rawar gani wajen ingiza gudanar da aikin daidaita wannan batu cikin adalci da daidaito.
Bugu da kari, Mao Ning ta ce, Sin da Amurka na kara tuntubar juna game da ci gaba da sa hannu kan yarjejeniyar hadin kan kasashen biyu, game da batun raya kimiyya da fasaha. Ta ce, kafa shinge ga bunkasuwar kimiyya ba zai dakatar da ci gaban kirkire-kirkire da Sin take gudanarwa ba. (Amina Xu)