Har kullum, Amurka ta kasance mai kokarin dora alhakin muggan laifukan da ake aikatawa a kasar kan wasu, maimakon lalubo tushensu domin samar da mafita mai dorewa.
A kokarin ci gaba da nuna kiyayya da yada jita-jita don bata sunan kasar Sin, a baya bayan nan, shugaban Amurka Joe Biden ya sanya kasar Sin cikin wasu jerin kasashe da ya bayyana a matsayin masu samarwa ko safarar miyagun kwayoyi.
Da farko dai, ba ni kadai da na shafe shekaru sama da 5 a kasar Sin ba, har da sauran baki da suka zauna ko ziyarci kasar, za su iya shaida cewa wannan zargi ya saba da ainihin yanayin da ake ciki a kasar. Kowa ya san cewa, safara ko amfani da miyagun kwayoyi a kasar Sin, babban laifi ne da zai fuskanci fushin doka.
Wani abu da kan burge ni da kasar Sin shi ne, yadda a ko da yaushe, ba ta kasa a gwiwa wajen daukar tsauraran matakan yaki da duk wani mugun abu ko muguwar tabi’a da za su iya lahanta moriyar al’ummarta, ciki kuwa har da tu’ammali da miyagun kwayoyi da safararsu.
Abun takaici ne yadda Amurka ta kasa gane cewa, rashin ingantattu matakai da suka kamata da rashin mayar da hankali kan al’ummarta ne tushen matsalolinta. Maimakon ta rika lalubo hanyoyin kyautatawa al’umma da kare su, sai ta bata lokaci wajen dora laifinta kan wata ko wasu kasashe. Lamarin da yake kara nuna rauninta na jagoranci da irin jan aikin dake gabanta.
A ganina, ko a wannan fanni ma, ya kamata Amurka ta yi koyi da dabarun kasar Sin kan yadda take yaki da miyagun kwayoyi da irin gudunmawar da ta bayar a wannan fanni a duniya.
Idan ba a manta ba, kasar Sin ce kasa ta farko a duniya da ta sanya kwayar fentanyl da ma abubuwan da suke da alaka da ita cikin jerin miyagun kwayoyi, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen hana samarwa da safara da ma shan kwayar, don haka, bai kamata Amurka ta rika alakanta kasar Sin da safarar ko samar da miyagun kwayoyi ba, wannan wani salo ne na cin zali. (Faeza Mustapha)